Matsalolin Nijeriya za su gushe ba da daɗewa ba – Idris

Daga BASHIR ISAH

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri sannan samu yaƙini game da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda ƙoƙarin da take yi wajen magance matsalolin da suka addabi ƙasa.

Idris ya ce gwamnati na aiki ba dare ba rana wajen daidaita lamurran ƙasa, tare da cewa za a shawo kan ƙalubalenbda suka addabi ƙasa nan ba da daɗewa ba.

Ministan ya yi wannan kira ne a wajen taron buɗe-baki tare da ‘yan jarida wanda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa ta shirya a cibiyar Armani Event Center da ke Kano a ranar Laraba.

Ya ce, Shugaba Tinubu ya gabatar da ingantattun tsare-tsare da shirye-shiryen da za su bunƙasa walwalar ‘yan Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, ya kamata ‘yan Nijeriya su samu ƙwarin gwiwa kan gwamnatin Bola Tinubu domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsaren da ta shimfiɗa.

Ya ce, domin bai wa ‘yan jarida damar yaɗa bayanan gwnati yadda ya kamata, za a samar da zarafin bafa horo da kuma kayan aiki irin na zamani.

Haka nan, ya ce gwamnatin Tinubu ta ba da himma wajen farfaɗo da matatun mai da ake da su a ƙasa, yan mai cewa nan da wani ɗan lokaci za a kamma gyaran matatar mai ta Fatakwal don a soma amfani da ita.

Kazalika, Ministan ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da yadda gwamnatin baya ta tafiyar da Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce gwamnati Tinubu ta yi ƙoƙari wajen dawo da martabar Bankin ta hanyar samar da tsare-tsare da dokoki nagartattu.