‘Ban fuskanci wata matsala ba wajen sauya jinsina’ – Bobrisky

Daga BASHIR ISAH

Matashin ɗan Nijeriyar nan da ya sauya jinsinsa zuwa mace, wato Bobrisky, ya ce komai ya tafi daidai na aikin sauya masa jinsi da aka yi daga namiji zuwa mace.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Bobrisky ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka yi masa aiki cikin nasara, yana mai cewa babu wata matsala da ya fuskanta a yayin aikin.

A cikin saƙon nasa, ya bayyana godiyarsa ga likitocinsa na gida da ƙetare bisa ƙoƙarin da suka yi wajen sauya masa jinsi zuwa mace.

Majiyarmu ta rawaito Bobrisky na cewa, “Komai na tafiya dadai game da batun sauya jinsina zuwa mace, babu wata matsalar rashin lafiya.

“Ina godiya ga likitocina na gida ƙetare. Baki ɗayanku kun taka rawar gani wajen yi mini aiki,” in ji shi.