Adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya ƙaru zuwa 31,819 — Abu Shawesh

Daga BASHIR ISAH

Ofishin jakadancin Falasɗin a Nijeriya, ya bayyana cewa yazu ran Laraba, 20 ga Maris, 2024 adadin Falasɗinawa da aka kashe Gaza ya kai 31,819, yayin da 73,934 sun jikkata, sannan kimanin mutum 8,500 sun ɓace ba tare da an san inda suke ba.

Jakadan Falasɗin a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, shi ne ya bayyana haka a cikin sanarwar manema labarai da ya fitar ranar Alhamis.

Jakadan ya ce baya ga kisan kiyashi da yankin Gaza ke fuskanta daga Isra’ila, yankin na kuma fama da matsanancin ƙarancin abinci, wanda a cewarsa wannan shi ne irinsa na farko da aka samu wata al’umma ta fuskanci matsalar rashin abinci makamancin haka.

Ya ce, “Kashi 100 cikin 100 na Al’ummar Gaza na fuskantar matsanancin ƙarancin abinci, wanda wannan shi ne irinsa farko da aka taɓa samun wata al’umma ta yi fama da hakan.”

Ya ƙara da cewa, “Ya zuwa ranar Laraba, 20 ga Maris 20, adadin Falasɗinawa da aka kashe ya kai 31,819, yayin da 73,934 sun tagayyara, sannan kusan mutum 8,500 sun ɓace.

“Akwai ‘yan gudun hijira 700,000 da suka fake a kashi 20% kacal na yankin Zirin Gaza.”

Haka nan, sanarwa ta rawaito Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, na cewa: “Falasɗinawa a yankin Gaza na shan baƙar wahala da yunwa, wannan shi ne adadi mafi yawa na jama’a da aka taɓa samu sun fuskanci bala’in yunwa ko’ina a kuma kowane lokaci.”

Bugu da ƙari, sanarwar ta rawaito babban jami’in sashen kula da ‘yancin ɗan’adam na MƊD, Volker Türk, na cewa, “Yunwa da wahalhalunnda ake fama da su a Gaza, hakan ta faru ne sakamakon hana shiga da magunguna, kayayyakin abinci da sauran kayayyakin tallafi da Isra’ila ta yi.”

Ofishin jakadancin ya ce kimanin kwanaki 167 ke nan da Isra’ila ta fara yi wa al’ummar Gaza kisan kyashi.