Amusan ta lashe tambarin zinare a gasar tseren Afrika

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sarauniyar wasannin guje-guje ta Nijeriya, Tobi Amusan, ta cika burin magoya bayanta bayan da ta lashe tambarin zinare a tseren gudu na mita 100 a gasar kofin Afrika da ke ci gaba da gudana a ƙasar Ghana.

Amusan, wadda ita ce ke riƙe da kambun tseren mita 100 na duniya, ta kasance wadda aka fi so a gasar, an nuna mata ƙauna bayan ya doke sauran abokan hamayyarta a karo na farko a tsaren.

A karo na biyu bayan an harba bindigar farawa, Amusan ba ta tsaya sanya ba, inda ta yi nasara a cikin sauƙi a daƙiƙa 12.89.

Nasarar na nufin ’yar wasan na Nijeriya ta yi “ci uku a jere” a gasar kofin Afirka, bayan da ya lashe kofi biyu na ƙarshe a Congo Brazzaville da Rabat.

Wata ‘yar wasan Nijeriya da ta fafata a gasar Faith Osamuyi, ta kasa samun nasara a gasar bayan ta yi tseren 13.77 a matsayi na huɗu.