Tinubu zai tsige ministocin da suka gaza kataɓus

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu yana shirin fara wani tsari mai matakai uku domin tantance ƙoƙarin ministoci, shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Manufar ita ce samar da wani shafi da zai ba jama’a damar yin bayanai game da koƙarin ministocin da ba da shawarar waɗanda za a riƙe da waxanda za a kora.

Wannan yunkuri na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tinubu ke tunkarar bikin cika shekara gyda a kan madafun iko a ranar 29 ga Mayu, 2024.

Wasu majiyoyi masu ƙarfi a fadar shugaban kasa sun ce Shugaban kasar Tinubu zai ƙaddamar da wannan shafi ne a ranar Talata, 19 ga watan Maris.

A cewar majiyoyin wannan shafi zai ba ‘yan Nijeriya damar faɗin ra’ayoyinsu kan ayyukan ministoci da kuma ƙoƙarin da suka yi.

Sai dai an ɗage buɗe shafin zuwa makon gobe domin ba ofishin mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsare karƙashin jagorancin Hadiza Bala-Usman damar kammala aikin.

A cewar Hadiza Bala-Usman, za a ɗauki matakin sauke ministocin da ba su yi aikin da ya kamata ne ta hanyar bin muhimman matakai guda uku.

Waɗannan matakai su ne;

  1. Ra’yoyi da tantancewar ‘yan Nijeriya.
  2. Hannun ofishin kula da tsare-tsare.
  3. Tawagar masu bada shawari za su tantance ayyuka da ƙokarin kowane minista zuwa yanzu.

“Saboda haka waɗannan za su zama ginshiƙin tantance ko wane minista da zai cigaba da aiki da waxanda za a tsige saboda sun gaza,” inji Hadiza.