Kayan miliyoyin Naira sun kone a gobarar kasuwar Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kayayyaki da darajarsu ta kai na miliyoyin Naira sun kone kurmus a ranar Larabar da ta gabata, yayin da wata gobara ta tashi a wasu shaguna a sashen Nnamdi Azikiwe da Docemo na Kasuwar Idumota a Jihar Legas.

Gobarar ta shafi gine-gine guda uku da suka haɗa da benaye biyu da wani gini mai hawa uku a kasuwar waɗanda suka shahara  wajen sayar tufafi da jaka da takalma.

Hukumar kashe gobara ta jihar Legas da sauran masu bada agajin gaggawa sun isa wurin, inda suka yi ta koƙarin aikin kashe gobarar.

“Hukumomin kashe gobara a Ebute Elefun, Ilupeju da Alausa sun tura kayan aiki don shawo kan lamarin yadda ya kamata yayin da ake ci gaba da kashe gobara,” inji shugabar hukumar kashe gobara, Margaret Adeseye.

“Har yanzu ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba, kuma ana ci gaba da bincike. Har yanzu ba a tabbatar da asarar rayuka ba.”

Adeseye ya buƙaci mazauna yankin da su ba jami’an agajin gaggawa haɗin kai tare da kaucewa yankin domin kare lafiyarsu.