Gina al’umma: Tsakaninmu da Gwamna Buni sai godiya – Hon. Lawan Bukar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Bursari a Jihar Yobe, Hon. Lawan Bukar ya bayyana cewa ba su da abinda za su ce wa gwamnan jihar Mai Mala Buni sai sam-barka, domin a cewarsa yana iyakacin ƙoƙarinsa na ganin ya sauke nauyin da al’ummar jihar ta ɗora masa.


Bukar ya ce Gwamna Buni ya tallafa wa kananan hukumomin jihar wajen ƙarfafa wa da inganta rayuwar jama’a musamman masu ƙaramin ƙarfi da gidajen marayu; samar da aikin yi ga matasa a ƙaramar hukumar Bursari da suka haɗa da: Samar da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a cikin birni da karkara tare da samar da magunguna a cibiyoyin kula da lafiya don yin rigafi ga cututtuka wanda ba a fata.

Ya ce Buni ya gyara da samar da rijiyoyin burtsatse a cikin birni da qauyukan karamar hukumar Bursari da sauran ƙananan hukumomi 17 da ke jihar ƙarƙashin shirin sabunta bege na maigirma gwamna. Kana ya samar da ingantattun kayan koyo da koyarwa a makarantar firamare da sakandare ta Bursari.
“Gyaran makarantu a garuruwa daban-daban da ƙauyuka da tanadin teburan zama a makarantun firamare da kuma ɗaukar ƙwararrun malamai masu shaidar digiri da NCE domin yara su samu nagartaccen ilimi.

“Samar da ingantaccen ruwan sha ta hanhar tona rijiyoyin burtsatse da gyara waɗanda suka ɓaci.

“Kimanin rijiyoyin burtsatse 46 da ke amfani da hasken rana a unguwanni 10 da tona rijiyoyin burtsatse 16 zuwa na zamani bi da bi a gundumomi 10 na ƙaramar hukumar,” inji Hon. Bukar.

Ɓangaren tsaro kuwa, Shugaban ƙaramar hukumar ya ce su da masu ruwa da tsaki suna samun damar sasanta rikicin makiyaya da Fulani bisa ƙudirin maigirma gwamna na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, wanda ya sun samu goyon baya ta hannun tsohon shugabansu kuma a halin yanzu ɗan jam’iyyarsu mai wakiltar Bursari a majalisar jiha Alh. Zannah Baba Dalami.

Inda suka sayo motoci da na’urori ga jami’ansu don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin ganawa akai-akai da shugaban hukumomin tsaro na qaramar hukumar da suka haɗa da ‘yan sanda, ‘yan banga na soji, hakimai, daggatai da sauran masu ruwa da tsaki.

Hon. Lawan Bukar ya ce Gwamna Buni ya bada kwangilar kasuwanni na zamani a ƙananan hukumomi 6 na jihar da suka haɗa da ƙaramar hukumar Bursari, kasuwar Bursari tana da girman ɗaukar mutane 30,000 da kuma gina kasuwar shanu a Alƙali wanda zai ɗauki shanu har 30,000 domin bunqasa kasuwanci a yankin.

Da yake magana kan Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas NEDC, Bukar ya ce sun yi matukar farin ciki da kafa hukumar wanda tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wanda kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ta 9, Sanata Ahmed Lawan ya yi ruwa ya yi tsaki wajen ganin ta tabbata, wanda kuma a cewarsa an samu ci gaba ta fuskoki da dama.

Hakazalika ya ce akwai ɗumbin shirye-shirye da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ke yi wajen kawo wa matasan yankin ci gaba ta hukumar NEDC.

Da ƙarshe ya yi kira ga matasan ƙaramar hukumar Burasari a kodayaushe ya kamata su mutunta kundin tsarin mulki sannan kuma su mutunta dattijai a cikin al’ummarsu kasancewar su ne shugabanni gobe.