Sarari ya ɗaukaka darajar MOPPAN zuwa ƙololuwa, inji Habibu Barde

“Muna son samar da tsarin shugabancin da zai saita masana’antar Kannywood”

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Alhaji Habibu Barde Muhammad shi ne sabon shugaban haɗaɗiyar ƙungiyar kwararru ta masu shirya fim ta ƙasa, wato MOPPAN, da ya kama mulki bayan saukar da tsohon shugaban Dakta Ahmad Muhammad Sarari ya yi a ƙarshen watan Janairun da ya gabata, wanda kafin hakan shi ne mataimaki na Arewa ta Tsakiya . Domin jin wanene Habibu Barde Muhammad da kuma irin gudunmawar da ya bayar a harkar fim, jaridar Blueprint Manhaja ta tattauna da shi, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance.

MANHAJA: Kafin kasancewar ka shugaban ƙungiyar ƙwararru ta masu gudanar da harkar fim wato MOPPAN za mu so ka ɗan yi wa masu karatu bayani a game da gudunmawar da ka bayar a cikin harkar fim da kuma abubuwan da ka sa a gaba a yayin gudanar da jagorancin ka na tsawon shekara guda da za ka yi nan gaba.

HABIBU BARDE: To ni dai na fara harkar qungiyoyin diramar Hausa a Bauchi tun 1979 bayan sakandare da BACAS ƙarƙashin ‘Bauchi state theater group’ na zamanin.

Na fara aiki a matsayin ‘Assistant producer’ a Bauchi Radio Corporation’ a 1980. Na tafi ‘Columbia College Hollywood ƙaro ilmi, a inda na yi diploma a ‘Television Radio productions’ a 1983. Na yi B. A. ‘Degree’ na gama a 1985 a Television/ Radio productions,’. Na dawo gida na yi NYSC a NTA ‘Television College’ na gama Disamba 1986. Na koma BRC Bauchi aiki Janairu 1987 ‘as Producer 2.’

Daga bude ‘Bauchi state Television Authority’ an maida ni wajen ”as producer one’ a 1989. Janairu 1990 Hukumar Mamsa wato NOA yanzu ta ɗauke ni aiki a hedikwatar ta a Abuja ‘as Senior Information officer’ mai shiryawa da gabatar da shirye shiryen su na wayar da kan jama’a  Radio Nigeria kaduna.

Na bar NOA na koma ‘main Federal Service as Assistant Chief Administrative Officer a presidency council Secretariat’ a Nuwamba. 1998. Na yi aikin ‘Administration on posting to’ maaikatun gwamnatin tarayya kamar, ‘culture and Tourism as P. A. to the permanent Secretary. Ministry of Agriculture, Defence Ministry under joint services Department special services section’ na tsawon shekara biyar daga 2004 zuwa 2009.

An maida ni mataimakin darakta a ‘Federal ministry of Youth Development’ bayan na kammala ‘Masters Degree’ a ABU Zaria a fannin ‘International affairs and Diplomacy’.
Bayan shekaru aka maida ni ‘Federal Ministry of Interior Business and citizenship Dept’ a matsayin mataimakin darakta. 2014 aka maida ni ‘Federal Ministry of Transportation Maritime Services Department’ a inda na yi ritaya a ‘Directorate Cadre level’ a watan Maris 2019, wanda ya yi daidai da shekaru na 59, hakan na nufin na yi wa qasata aiki na tsayin 35.

Kuma a duk tsawon wannan lokacin kuma ina harkar ‘Television and Radio’ tare da abokai na yi a Kannywood.

Yanzu bayan ina gudanar da ayyukan ‘productions’ na wani ‘Radio da Television’ ƙarƙashin kamfanina Hashwannar Nig Ltd a nan Abuja da Kano. Shi ne yanzu BOT ta MOPPAN ta  naɗa ni a matsayin sabon shugaban MOPPAN na ƙasa zuwa lokacin da za a yi zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar na kiasa a shekara mai zuwa in sha Allah.

Da yake shekara ɗaya ya rage maka za ka yi ko me ka shirya za ka gudanar a ckin shekarar?

To daman da ni aka gudanar da shugabancin na shekara biyu Ina matsayin mataimaki na Arewa ta Tsakiya, don haka duk da ni ake gudanar da komai, kuma Alhamdulillahi Dakta Ahmad Muhammad Sarari ya ɗaukaka darajar MOPPIN ya kai ta ƙiololuwa don haka duk abin da za mu yi sauran abin da ya rage ne, saboda shi jajirtaccen shugaba ne abin da za mu yi shi ne za mu tsara zaɓe wannan ya a sa ma a yanzu na zo Kano mun yi zama na Majalisar Ƙoli ta MOPPAN din wanda muka tattauna a kan yadda za mu gudanar da ayyukan da za mu yi cikin shekara guda ɗin da aka ba mu.

Kuma daman na faɗa maka za mu ƙarasa shekarar da shi Dakta Ahmad Muhammad Sarari ne, to amma kowanne shugaba akwai wani tsari da yake da shi wajen gudanar da nasa shugabancin don haka akwai wasu kudurori da ba zu gudanar wajen namu shugabancin don haka mun zaɓo wasu jigajigan mutane daga kowanne ɓangare na jihohin da muke da su domin tsara yadda za a samar da yanayin da za a gudanar da zaɓe da kuma yadda za mu ɗaukaka MOPPIN ɗin yadda shugabanni da za su zo su same ta a kan saiti.

Sannan mun samar da kwamitin gyara tarbiyyar ‘yan wasa duk da sauran kwamitocin za mu yi aiki na wata uku mu zagaya ƙasar nan domin gudanar da ayyukan mu da neman kuɗin da za mu gudanar da zaɓen da za mu yi da kuma kawo gyara a cikin masana’antar kuma Alhamdulillahi ina da karfin gwiwa a game da ‘yan kwamitin da za mu yi aiki da su masu kishin harkar ne masu son ganin gyaran ta ne kuma ni a matsayina na shugaba Ina son ne kawai na gudanar da zaɓe don ba ni da niyyar na tsaya takara saboda ina da wasu ayyuka na da nake buƙatar na gudanar, kuma ga shekaru na a yanzu sun kai na tsaya na huta na samu ishasshen lokaci don haka na ce da su ba zan nemi wata takara nan gaba ba zaɓe kawai zan tsara mu ga mun samar da tsari mai inganci da zai saita masana’antar kuma in Allah ya yarda ba zan zo na nema ba. Duk yadda aikin ya yi mini daɗi a haka zan bar shi don na je na samu hutu tare da gudanar da ayyukan da suke gabana.

A yanzu wanne buri kake da shi a tsawon shugabancin da za ka yi na shekara guda?

To gaskiya burina na samar da tsarin zaɓe mai kyau yadda za a samu shugabancin da za a ji daɗin sa wanda hakan zai sa a rinka tunawa da ni a tarihin masana’antar.

Kuma da tabbacin zan yi hakan da fatan samun goyon baya ga waɗanda za mu yi aiki tare don ganin ai kai ga cimma wannan buri da nake da shi.

To Madalla mun gode.

Ni ma na gode.