DMO ta fara sayar da takardun zuba jari na Gwamnatin Tarayya kan N1,000

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Basussukan Gwamnati (DMO) ta sanar da fara sayar da sabbin Takardun Bashin Ajiya na Gwamnatin Tarayya, wato FGN Savings Bonds, guda biyu, inda aka ƙayyade mafi ƙarancin farashin kowace guda kan Naira 1,000 domin bai wa talakawa da masu ƙaramin jari damar saka hannun jari.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a madadin Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa takardar bashi ta farko tana da wa’adin shekara biyu, wadda za ta ƙare ranar 12 ga Agustan 2028, tare da ribar kashi 13.96 cikin 100 a duk shekara.

Sannan takardar bashi ta biyu tana da wa’adin shekara uku, wadda za ta ƙare ranar 12 ga Agustan 2029, kuma za ta biya ribar kashi 14.96 cikin 100 a duk shekara.

DMO ta ce an fara karɓar buƙatun sayen takardun bashin ne daga ranar Litinin, yayin da za a rufe sayayya ranar 7 ga Agusta. Za a kammala cinikin kuma a raba takardun bashin ranar 12 ga Agusta.

Hukumar ta ƙara da cewa za a rika biyan ribar masu saka hannun jari sau huɗu a shekara, wato a ranakun 12 ga Nuwamba, 12 ga Fabrairu, 12 ga Mayu da 12 ga Agusta, yayin da za a mayar da cikakken kuɗin jari idan wa’adin takardar ya cika.

A cewar DMO, ana sayen kowace takardar ne daga Naira 1,000, amma mafi ƙarancin adadin da mutum zai iya saka shi ne Naira 5,000, sannan ana iya ƙara saka jari da Naira 1,000-1,000 har zuwa iyakar Naira miliyan 50.

Hukumar ta tabbatar da cewa dukkan Takardun Bashin Ajiya na Gwamnatin Tarayya suna da cikakken goyon bayan gwamnatin ƙasa, kuma an tabbatar da su da dukiyoyin gwamnatin Nijeriya. Ta kuma bayyana cewa dokokin ƙasa sun amince da waɗannan takardun a matsayin hanyoyin saka hannun jari da amintattu, waɗanda amintattun masu kula da kadarori za su iya amfani da su.

Haka kuma, takardun bashin suna cikin kadarorin gwamnati da ke samun wasu rangwamen haraji ga wasu masu saka hannun jari, ciki har da asusun fansho, kamar yadda dokokin harajin kamfanoni da na harajin kuɗaɗen shiga na mutane suka tanada.

DMO ta ce an yi rajistar Takardun Bashin Ajiya na FGN a Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGɗ), kuma bankuna na iya amfani da su wajen ƙididdige yawan kadarorin ruwa da ake buƙata a tsarin gudanar da harkokinsu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa an ƙirƙiri Takardun Bashin Ajiya na FGN ne domin bai wa masu ƙaramin jari da masu karɓar albashi damar saka kuɗinsu cikin takardun bashin gwamnati ba tare da buƙatar manyan kuɗaɗen da ake buƙata wajen sayen sauran nau’ikan takardun bashin Gwamnatin Tarayya ba.

Saka kuɗi a irin waɗannan takardun bashi na nufin mutum ya ba Gwamnatin Tarayya rance, wadda za ta riƙa biyansa riba a kai a kai har zuwa lokacin da wa’adin takardar zai cika, sannan ta mayar masa da cikakken kuɗin da ya saka.

By ukarofi

Leave a Reply