Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fadar Shugaban ƙasa ta mayar da martani mai zafi ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, inda ta kare manufofin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa sukar da Atiku ke yi ta ginu ne kan tsofaffin bayanai da ba sa nuna ainihin halin da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki a halin yanzu.
Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai taken “Gaskiya Ce, Ba Tsoratarwa Ba: Fadar Shugaban ƙasa Ta Yi Martani Dalla-dalla Kan Sukan Atiku Game da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya”, inda ya ce Atiku ya taƙaita hukuncinsa kan gwamnatin ne bisa irin ƙalubalen da aka fuskanta a shekarar 2024, ba tare da la’akari da ci gaban da aka samu cikin shekaru biyun da suka gabata ba.
Ya ce, siyasa tana bai wa mutane damar saɓani, amma ya kamata irin wannan saɓani ya kasance bisa hujjoji da sahihan bayanai, ba tsofaffin alƙaluma ba.
Da yake mayar da martani kan zargin da Atiku ya yi na almubazzaranci da kuɗin gwamnati, yawan bashin ƙasa da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki, Onanuga ya ce ba daidai ba ne a auna tasirin sauye-sauyen gwamnati da wahalolin farkon aiwatar da su kawai.
Ya ce, bayan da aka sake fasalin canjin kuɗi a 2024, darajar tattalin arzikin Nijeriya da ake aunawa da dalar Amurka ta ragu zuwa kusan dala biliyan 253, amma yanzu ta ƙaru zuwa kusan dala biliyan 377, abin da ya nuna ƙarin kusan kashi 49 cikin ɗari.
Haka kuma ya ce darajar tattalin arzikin ƙasar da naira ta tashi daga kusan naira tiriliyan 314 zuwa kusan Naira tiriliyan 530.
Onanuga ya ce ba yawan bashin ƙasa kaɗai ake dubawa wajen tantance lafiyar tattalin arziki ba, illa ana la’akari da girman tattalin arzikin ƙasa, ƙarfin samun kuɗaɗen shiga, nauyin biyan bashi da kuma inda ake amfani da kuɗin da aka aro.
A cewarsa, rabon bashin Nijeriya da tattalin arzikinta bai kai kashi 40 cikin ɗari ba, yayin da kuma rabon kuɗin biyan bashi da kuɗaɗen shiga ya sauka daga kusan kashi 100 cikin ɗari a ƙarshen shekarar 2022 zuwa ƙasa da kashi 60 cikin ɗari a halin yanzu.
Fadar Shugaban ƙasa ta ce cire tallafin man fetur na daga cikin manyan matakan gyaran tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka.
Onanuga ya ce gwamnatocin baya, har da wadda Atiku ya yi mataimakin shugaban ƙasa a cikinta, sun kasa cire tallafin duk da sanin irin illar da yake yi wa tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa, cire tallafin ya ƙara kuɗaɗen da jihohi da ƙananan hukumomi ke samu daga Asusun Tarayya, lamarin da ya ba su damar ƙara kashe kuɗi wajen gina hanyoyi, makarantu, asibitoci, biyan albashi da fansho da kuma gudanar da shirye-shiryen jinƙai.
Game da zargin ƙarin haraji, Onanuga ya ce manufar gyaran tsarin haraji ba wai ƙara tara kuɗi kawai ba ce, sai dai samar da tsarin da ya fi adalci.
Ya ce tsarin ya rage wa masu ƙaramin ƙarfi haraji, musamman masu samun ƙasa da naira miliyan ɗaya a shekara da kuma ƙananan kamfanonin da kuɗin shigarsu bai wuce naira miliyan 100 a shekara ba.
Fadar Shugaban ƙasa ta ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori a ɓangarorin lafiya da ilimi.
A cewarta, an gyara cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko sama da 3,000, an sake horas da ma’aikatan lafiya sama da 78,000, yayin da cibiyoyi fiye da 100 ke gudanar da tiyatar haihuwa kyauta ga mata marasa galihu.
Ta kuma ce an buɗe cibiyoyin kula da masu cutar kansa a Kubwa, Enugu da Katsina, tare da faɗaɗa irin waɗannan cibiyoyi a wasu jihohi 13.
A ɓangaren ilimi kuwa, gwamnatin ta ce ta aiwatar da fiye da ayyuka 11,000 ta hannun Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta ƙasa (UBEC) tare da gwamnatocin jihohi.
Haka kuma ta ce Asusun Ba da Lamunin Karatu na Nijeriya (NELFUND) ya tallafa wa ɗalibai sama da miliyan 1.64, inda aka fitar da sama da naira biliyan 303 ga cibiyoyin ilimi sama da 300.
Onanuga ya kuma yi watsi da zargin Atiku cewa gwamnati ta samu wata boyayyiyar ribar Naira tiriliyan 7.98 daga sayar da ɗanyen mai.
Ya ce duk da cewa farashin mai ya haura hasashen kasafin kuɗi a rabin farkon shekarar 2026, ƙarancin yawan man da ake haƙowa ya rage kuɗin da gwamnati ta samu.
A cewarsa, matsakaicin haƙon mai ya kai ganga miliyan 1.6 a rana, ƙasa da ganga miliyan 1.84 da aka tsara a kasafin kuɗi.
Dangane da hauhawar farashi, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce mafi tsananin matsin rayuwar da sauye-sauyen tattalin arziki suka haifar ya riga ya wuce.
