Gwamnatin Nijeriya ta sha alwashin inganta tsarin lantarki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da samar da ingantacciyar wutar lantarki ga ‘yan Nijeriya, inda ta bayyana shirinta na zuba sabon jari domin ƙarfafa tsarin Grid na Wutar Lantarki na ƙasa, da nufin kawo ƙarshen yawaitar rushewar tsarin da kuma matsalar sauyin ƙarfin lantarki.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa ma’aikatar ta fara ɗaukar matakan da suka wuce gyare-gyaren gaggawa, inda ta mayar da hankali kan sake fasalin tsarin wutar lantarki gaba ɗaya.

A cewarsa, tabbatar da daidaiton grid shi ne ginshiƙin da zai ba da damar cika duk wasu alkawuran da gwamnati ta ɗauka na inganta harkar wutar lantarki.

Ya ce, “Ba za a iya magana kan ƙara yawan samar da wuta ko gyaran tsarin rarraba ta ba idan grid ɗin kansa yana cikin rauni. Wannan gwamnati ta himmatu wajen gina grid mai ƙarfi da ɗorewa, ba kawai a matsayin alƙawari ba, amma a matsayin shiri mai takamaiman manufofi da jadawalin aiwatarwa.”

A wata sanarwa da aka fitar, Ma’aikatar Wutar Lantarki ta ce an kafa Kwamitin Fasaha Kan Daidaita Grid domin jagorantar wannan shiri. Kwamitin zai haɗa ƙwararrun injiniyoyi da masana harkokin tsare-tsare domin magance matsalolin da suka dabaibaye tsarin isar da wutar lantarki, ciki har da tsofaffin kayayyakin aiki da kuma yawan rushewar tsarin da ke jefa al’umma cikin katsewar wuta.

An kuma bayyana cewa kwamitin zai yi aiki tare da Kamfanin Isar da Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) da kuma Hukumar Kula da Tsarin Gudanar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NISO) wajen gano muhimman wuraren da ke buƙatar gyara cikin gaggawa.

Jami’ai sun ce sabon jarin zai mayar da hankali ne kan ƙarfafa manyan hanyoyin isar da wutar lantarki, samar da madadin hanyoyin gudanar da grid idan aka samu matsala, tare da sabunta tsarin sa ido da sarrafa grid domin rage yawaitar katsewar wuta.

Wannan mataki ya zo ne yayin da Ma’aikatar Wutar Lantarki ke ƙoƙarin dawo da amincewar jama’a kan ɓangaren, bayan shekaru ana fama da matsalolin katsewar wuta da kuma rashin cika alƙawuran da aka sha yi a baya.

Ministan ya amince cewa mutane da dama sun rasa kwarin gwiwa saboda alƙawuran da ba su cika ba, yana mai cewa gwamnatin yanzu ta fahimci cewa abin da zai sa a yarda da ita shi ne sakamakon ayyukanta, ba furuci kaɗai ba.

Ya ce, “Ba ma neman mutane su gaskata mu ba tare da hujja ba. Muna so a riƙa auna mu da irin ci gaban da za mu samu bisa manufofin da muka shimfiɗa, kuma hakan ne muka ƙuduri aniyar yi.”

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa za ta riƙa sanar da jama’a matakai da ci gaban da ake samu kan shirin daidaita grid, domin masu ruwa da tsaki, masu zuba jari da sauran ‘yan ƙasa su kasance suna samun sahihan bayanai cikin lokaci.

By ukarofi

Leave a Reply