Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana goyon bayansa ga sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa tare da yaba wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) kan matakan da ya ɗauka, domin daidaita tattalin arzikin ƙasar.
Sarkin, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya ne, ya ce, ƙasar ta kauce wa mummunar barazanar durƙushewar tattalin arziki sakamakon matakan da aka ɗauka na rage yawaitar kuɗaɗen da suke yawo a kasuwa, daƙile hauhawar farashi da kuma daidaita darajar Naira.
A yayin da yake magana kan halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, Sanusi ya ce ba shi da abin da zai ce face yabawa ga irin aikin da Babban Bankin Nijeriya ya yi.
A cewarsa, Nijeriya ta fito daga wani mawuyacin hali na rashin daidaiton tattalin arziki da ya samo asali daga yawaitar kuɗaɗe a kasuwa da rashin tsauraran matakan kula da manufofin kuɗi.
Sai dai ya ce CBN ya shafe shekara guda yana aiwatar da matakan rage yawan kuɗaɗen da ke yawo domin dawo da daidaito.
Sanusi ya amince cewa har yanzu kuɗin ruwa na rance yana da tsada, amma ya ce sauye-sauyen sun taimaka wajen daidaita darajar naira tare da inganta makomar tattalin arzikin ƙasar.
Ya ce, “Haƙiƙa kuɗin ruwa ya yi yawa, amma mun daidaita farashin canjin kuɗi, kuma mun kuɓuta daga barazanar durƙushewar tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.”
Tsohon gwamnan na CBN ya kuma ce duk da cewa hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da kasancewa mai yawa, ana samun raguwarsa idan aka kwatanta da matakan da ya kai a shekarun baya.
A cewarsa, “Har yanzu hauhawar farashi tana kusan kashi 20 cikin 100, wanda babu shakka yana da yawa, amma tana ci gaba da raguwa idan aka kwatanta da yadda take a shekarun baya.”
Sanusi ya kuma bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar na ƙasashen waje ya haura dala biliyan 40, lamarin da ya ce alama ce ta ingantuwar tattalin arzikin Nijeriya.
Bugu da ƙari, ya ce tattalin arzikin ƙasar ya samu ci gaba da ya zarce yawan haɓakar al’umma, yana mai bayyana hakan a matsayin wani gagarumin ci gaba.
Ya ce, “Tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da fiye da kashi uku cikin ɗari a farkon shekara, sannan ya haura kashi huɗu cikin ɗari a tsakiyar shekara. Wannan shi ne karon farko cikin shekaru masu yawa da tattalin arzikin Nijeriya ya fi saurin bunƙasa fiye da yawan haɓakar al’umma.”
