Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Sabuwar taƙaddama ta kunno kai kan mallakar Gandun Makanikai (Mechanics Village) da ke Gombe, bayan gwamnatin jihar ta ci gaba da rabon shaguna, rumfuna da wuraren ajiye kwantena ga masu sana’o’i, duk da wani hukuncin babbar kotun Jihar Gombe kan mallakar wani sashe na filin.
A hukuncin da Mai Shari’a Daurabo S. Sikkam ta yanke a ƙarar GM/116/2026, kotun ta amince da Emir General Integrated Limited a matsayin mamallakin wani fili mai girman hekta 1.30 da ke kan titin Gombe-Bajoga, kusa da ofishin NURTW.
Kotun ta kuma tabbatar da ingancin Certificate of Occupancy mai lamba GM/15926, tare da umartar gwamnati da sauran waɗanda ake ƙara da su su fice daga filin, sannan su cire gine-ginen da aka yi a wurin.
Bugu da ƙari, kotun ta bayar da Naira miliyan 15 a matsayin diyya ta musamman da Naira miliyan 50 a matsayin diyya ta gaba ɗaya, baya ga N7,200 na kuɗin shari’a, tare da ribar kashi 10 cikin 100 a duk shekara.
Sai dai bayan hukuncin, bincikenmu ya gano cewa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta Jihar Gombe ta raba wasu wurare a Gandun Makanikai ga ƙungiyoyin masu sana’o’i.
A rabon, NATA ta samu wuraren ajiye kwantena 500, rumfuna 60 da shaguna takwas.
Haka kuma, GATAL ta samu wuraren kwantena 220, rumfuna 27 da shaguna uku, yayin da ƙungiyar ’yan fanal bita ta samu wuraren kwantena 37, rumfuna biyar da shago guda.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu, Nasiru Muhammad Aliyu, ne ya jagoranci rabon wuraren.
Sai dai ba a fayyace ko wuraren da aka raba suna cikin filin hekta 1.30 da hukuncin kotun ya shafa ba, ko kuma wane tushe na doka aka yi amfani da shi wajen yin sabon rabon.
Lauyan Emir General Integrated Limited, Barista Sulaiman Abdurraheem, ya bukaci gwamnatin jihar ta aiwatar da hukuncin kotun, ciki har da biyan diyya da kuma cire gine-ginen da hukuncin ya shafa.
Ya ce idan gwamnati na son mallakar filin da ke da ingantacciyar takardar mallaka domin amfanin jama’a, dole ne ta bi matakan da doka ta tanada.
A nasa ɓangaren, lauyan gwamnatin jihar, Barista Musa Adamu Kumo, ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar sasanta batun a wajen kotu, sai dai bai yi ƙarin bayani kan matakin da gwamnati ke shirin ɗauka ba.
Shi kuwa Daraktan Grandscope Construction Company, Tanko Isiaku Gwamna, ya ce a tuntubi lauyan kamfanin, Barista Daniel Tsaro, domin jin matsayar kamfanin kan batun.
Sai dai Barista Tsaro bai bayar da ƙarin bayani ba har zuwa lokacin kammala rahoton.
Har ila yau, gwamnatin jihar da Ma’aikatun Ayyuka da Kasuwanci da Masana’antu ba su bayyana tushen doka da aka yi amfani da shi wajen rabon wuraren ba.
Hakan ya bar tambayoyi kan ko sabon rabon ya shafi filin da hukuncin kotun ya shafa, da kuma matakin da gwamnatin jihar za ta ɗauka wajen aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke.
