An yi wa basarake kisan gilla a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rahotanni daga garin Lafagu da ke ƙaramar hukumar mulki ta Bagudo a jihar Kebbi sun bayyana an kashe basaraken garin Alhaji Sai’du Sarkin Lafagu.

Wani mazauni garin Bagudo ya bayyanawa wakilin Jaridar Blueprint Manhaja da cewa daren ranar Asabar ɗin da ta gabata ne waɗansu mahara ɗauke da makamai suka yi dirar mikiya gidan basaraken inda suka nemi ya ya fitar da waɗansu Fulani da suke nema inda basaraken ya tabbatar musu da cewa shi ba ya da wani haɗi da waɗansu fulani.

Bayan sun azabtar da shi daga baya suka yi masa yankan rago tare da cire kan sa baki-ɗaya suka tsire.

Yanzu haka dai garin Bagudo ya cika maƙil da yan gudun hijira daga ƙauyukan da ke yankin sanadiyyar yawan hare-hare da kisan gilla da ake yi wa mutane a yankin inda ya kai ba maganar makarantu ba ne ko wani kangon gida ba yanzu haka mutane suna nan kan tituna suna gararamba saboda ba wajen kwana.

By ukarofi

Leave a Reply