Rikicin siyasa ya sake kunno kai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, inda ‘yan sanda suka tarwatsa zanga-zangar da masu adawa da gwamnati suka gudanar a birane da dama, domin nuna rashin amincewa da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar da ake takaddama a kansu.
A babban birnin kasar, Kinshasa, daruruwan mutane ne suka fito ranar Talata domin nuna adawa da sauye-sauyen, inda lamarin ya fara cikin lumana kafin daga bisani ya rikide zuwa arangama tsakanin masu zanga-zangar da magoya bayan gwamnati. Shaidun Reuters biyu da ke wurin sun ce ɓangarorin biyu sun rika jifan juna da duwatsu tare da daga adduna, abin da ya sa ‘yan sanda suka shiga lamarin tare da amfani da hayaki mai sa hawaye da harbe-harben gargadi domin tarwatsa jama’ar.
Zanga-zangar dai gamayyar ‘yan adawa ta C64 ce ta shirya, wadda ke da alaka da wasu daga cikin tsoffin ‘yan takarar shugaban kasar, ciki har da Martin Fayulu, Moise Katumbi da Delly Sesanga. A wasu biranen kasar kamar Lubumbashi da Uvira, hukumomin yankunan sun haramta zanga-zangar, amma masu adawa da gwamnati sun gudanar da ita duk da haka, kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.
Abin da ya fi jawo ce-ce-ku-ce shi ne sauyin kundin tsarin mulkin da ake son yi, wanda masu adawa da Shugaba Félix Tshisekedi ke cewa zai iya bude masa kofar sake neman shugabancin kasar karo na uku. Kundin tsarin mulkin Congo na yanzu ya takaita wa shugaban kasa wa’adin shekaru biyar-biyar biyu kacal, yayin da majalisar dattawan kasar ta amince da wani kudiri a watan Yuni da zai ba da damar kai sauye-sauyen kundin tsarin mulkin zuwa kuri’ar raba gardama.
Tshisekedi, wanda ke kan mulki tun 2019, ya kuma sanar a watan Agusta cewa yana son a gudanar da tattaunawar kasa tsakanin jam’iyyun siyasa, kungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai domin rage rikicin siyasar kasar. Sai dai an ware kungiyoyin ‘yan tawaye da ke iko da wasu yankunan gabashin kasar daga cikin wannan tattaunawa.
Ga ‘yan adawa, batun sauya kundin tsarin mulkin ya wuce batun gyaran doka kawai, domin suna kallon yiwuwar sauyin a matsayin matakin da zai iya sauya ka’idojin da ke takaita wa shugaban kasa wa’adi biyu. A daya ɓangaren kuma, gwamnatin Tshisekedi ta gabatar da tattaunawar kasa a matsayin hanyar da za a bi wajen tunkarar ƙalubalen siyasa da tsaro da kasar ke fuskanta.
Sabon rikicin ya zo ne a lokacin da Congo ke fama da wasu manyan matsaloli, ciki har da rikicin makamai a gabashin kasar da kuma annobar Ebola. Hakan ya kara sanya zanga-zangar da aka gudanar a birane daban-daban cikin wani yanayi mai sarkakiya, yayin da ake ci gaba da muhawara kan makomar kundin tsarin mulkin kasar da shugabancin Tshisekedi.
