EU na son Kanada ta zama mamba ta musamman a ƙungiyar

Spread the love

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai (EU), Ursula von der Leyen, ta ce tana son a buɗe ƙofa domin Kanada ta zama ƙasa ta farko da za ta samu matsayin “mamba ta musamman” a cikin ƙungiyar, a wani sabon yunkuri na ƙara ƙarfafa alaƙar Turai da ƙasar.

Von der Leyen ta bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da Firaministan Kanada, Mark Carney, ya halarci zaman Majalisar Tarayyar Turai a Strasbourg, inda ta gabatar da jawabin shekara-shekara kan halin da ƙungiyar take ciki. Bayan furucin nata, ‘yan majalisar sun tashi tsaye suna tafa mata, yayin da ita da Carney suka rungumi juna.

Ta ce yanayin duniya na yanzu na buƙatar ƙasashe masu ra’ayi iri ɗaya su sake duba yadda suke gina haɗin gwiwa, musamman a lokacin da Turai ke fuskantar yaƙi a kan iyakokinta sakamakon mamayar Rasha a Ukraine, yayin da ita da Kanada ke fuskantar matsin lamba a harkokin kasuwanci da sauran fannoni daga gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump da kuma ƙara ƙarfi da Chana ke yi a fagen duniya.

“Ya kamata mu gaggauta sake tunanin yadda muke gina alaƙarmu da abokan hulɗarmu. Don haka ina son mu yi aiki tare wajen buɗe ƙofa domin Kanada ta zama mamba ta musamman ta farko a EU,” inji von der Leyen.

Ta ce Turai da Kanada suna kallon duniya ta fuska iri ɗaya a wasu muhimman batutuwa, ciki har da fasahar AI, sauyin yanayi, yankin Arctic da siyasar duniya. Ta kuma ambaci haɗin gwiwar ɓangarorin biyu kan Ukraine, tsaro, albarkatun ƙasa da hanyoyin samar da kayayyaki, tana mai cewa abin da ya fi haɗa su shi ne imani da dimokuraɗiyya.

Sai dai ba ɓon der Leyen kaɗai ce za ta iya tabbatar da wannan shiri ba. Dole ne ƙasashe 27 da ke cikin Tarayyar Turai su amince da shi, kuma batun ya zo ne a lokacin da EU a tarihi ta kasance mai taka-tsantsan kan samar da wasu nau’ikan alaƙar zama mamba da ba su da cikakken matsayi a dokokin ƙungiyar.

Wani jami’in diflomasiyyar EU ya bayyana mamakinsa kan shawarar, yana cewa har yanzu ba a fayyace ainihin abin da matsayin “mamba ta musamman” zai ƙunsa ba. Ya kuma nuna damuwa kan ko Hukumar Tarayyar Turai za ta iya cika abin da aka yi alkawari.

Kafin jawabin von der Leyen, jami’an diflomasiyya bakwai na EU da ke Kanada da Turai sun shaida wa Reuters cewa ana gudanar da tattaunawa domin zurfafa haɗin gwiwar Kanada da ƙungiyar a harkokin kasuwanci, tsaro da tsaron fasahar sadarwa, amma ba a taɓa tattauna wani cikakken sabon tsarin alaƙa irin wanda von der Leyen ta gabatar a babban mataki ba.

A nasa ɓangaren, Carney ya ce Kanada na neman “ƙawance na musamman” da Tarayyar Turai, amma ba neman zama cikakkiyar mamba ba. Ya shirya yin nasa jawabi a Majalisar Tarayyar Turai ranar Alhamis.

By ukarofi

Leave a Reply