Babu dalilin da zai hana Arewa goyon bayan Tinubu a 2027 – Yari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Daraktan Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Abdul’Aziz Yari, ya ce babu wani dalili da zai hana al’ummar Arewa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarinsa na sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

Yari ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas, lokacin da ya jagoranci wasu mambobin kwamitin zuwa fadar Oba na Legas, Rilwan Akiolu.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasara a zaɓen 2015 da kuma sake zaɓensa a 2019.

Ya ce Tinubu ya ƙi matsin lambar da wasu daga cikin ’yan jam’iyyar APC suka yi masa na neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2019, inda ya ce lokacin Arewa ne ya kamata ta jagoranci ƙasar.

Yari ya ce saboda haka, lokaci ya yi da Arewa za ta rama wa Tinubu ta hanyar mara masa baya domin ya ci gaba da mulki.

“Babu wani uzuri da zai hana mu a Arewa goyon bayan Tinubu domin ya ci gaba da aikin alheri da ya fara, tare da kammala wa’adinsa,” in ji Yari.

Sanatan Zamfara ta Yamma ya ƙara da cewa akwai mutane masu nagarta da kishin adalci a Arewa da za su tabbatar da tafiyar Tinubu ta ci gaba har zuwa ƙarshe.

Yari ya kuma bayyana cewa Tinubu ya sake fasalin wasu abubuwa a ƙasar duk da ƙalubalen da ya gada daga gwamnatocin baya.

Ya ce kwamitin yaƙin neman zaɓen ba ya neman sake zaɓen Tinubu ne kawai bisa tsarin juyin mulki tsakanin Arewa da Kudu, sai dai saboda imanin cewa ’yan Nijeriya na son ya ci gaba da mulkin ƙasar.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya tarbi mambobin kwamitin kafin ya raka su zuwa fadar Oba, ya ce ziyarar da kwamitin ke kai wa sarakunan gargajiya na nuna muhimmiyar rawar da masarautun gargajiya ke takawa wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply