Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta ce, hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu kaɗan, inda ya koma kashi 15.39% a Agustan 2026, daga kashi 15.43% da aka samu a Yuli.
A cewar hukumar, hakan na nuna raguwar hauhawar farashin da maki 0.04 idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na Ma’aunin Farashin Kayayyaki (CPI) da ta fitar ranar Laraba.
NBS ta ce idan aka kwatanta hauhawar farashin kayayyaki daga wata zuwa wata, an samu kashi 0.71 cikin ɗari a Agustan 2026, wanda ya yi ƙasa da kashi 1.57 da aka samu a Yuli da maki 0.86. Hakan na nufin cewa matsakaicin hauhawar farashin kayayyaki a watan Agusta ya kasance a hankali fiye da yadda aka samu a watan Yuli.
A ɓangaren kayan abinci kuwa, NBS ta ce hauhawar farashin ya kai kashi 19.57 cikin ɗari a Agustan 2026 idan aka kwatanta da makamancin watan shekarar da ta gabata.
Sai dai wannan adadi ya yi ƙasa da kashi 25.30 da aka samu a watan Agustan 2025. Hukumar ta kuma ce idan aka duba sauyin farashin kayan abinci daga wata zuwa wata, an samu kashi 1.02 cikin ɗari a Agustan 2026, wanda ke nuna raguwar maki 4.55 daga kashi 5.56 da aka samu a Yuli.
A cewar hukumar, wannan na nuna cewa farashin kayan abinci na ci gaba da ƙaruwa, amma a hankali fiye da yadda ya kasance a watan Yuli.
NBS ta danganta raguwar hauhawar farashin kayan abincin da sauyin matsakaicin farashin wasu muhimman kayayyaki, ciki har da manja, karas, barkono, albasa, garin rogo, naman sa, garin doya, doyar ruwa, ƙuli-ƙuli na egusi, sabon citta, sabon kifi, dankalin Irish, hatsin alkama, kaji da naman talo-talo, da sauran kayayyaki.
Rahoton ya nuna cewa a Agustan 2026, jihar Adamawa ce ta fi samun hauhawar farashin kayan abinci idan aka kwatanta da makamancin watan shekarar da ta gabata, inda ta kai kashi 38.85 cikin ɗari. Zamfara ta biyo baya da kashi 37.96, yayin da Bayelsa ta kasance da kashi 36.20.
A ɗaya ɓangaren kuma, Borno ta samu mafi ƙarancin hauhawar farashin kayan abinci, inda aka samu raguwar kashi 4.04, sai Jigawa da raguwar kashi 0.23, yayin da Kebbi ta samu kashi 3.47 cikin ɗari. Idan aka duba sauyin farashin daga wata zuwa wata, Katsina ce ta fi samun hauhawar farashin kayan abinci, da kashi 9.48, sai Ribas da kashi 8.86, sannan Osun da kashi 8.32.
A gefe guda, Taraba ta samu mafi girman raguwar farashin kayan abinci, da kashi 12.42, sai Borno da kashi 12.15, yayin da Bauchi ta samu raguwar kashi 8.88.
