Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Haɓakar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya zuwa sama da dala 100 kan kowace ganga na ci gaba da haifar da tashin farashin man fetur a Nijeriya, lamarin da ya sanya manyan dillalan mai ƙara farashin da suke sayar da fetur a gidajen mai, tare da ƙara jefa masu sufuri, fasinjoji, gidaje da ’yan kasuwa cikin matsin tattalin arziki.
Kamfanin MRS ya ƙara farashin litar fetur daga N1,300 zuwa N1,400 a Legas da kewaye, wanda ke nufin ƙarin N100, kwatankwacin kashi 7.7 cikin 100.
Haka kuma, gidajen man da ke ƙarƙashin kamfanin NNPC Limited sun ƙara farashin litar fetur daga N1,275 zuwa N1,375, yayin da wasu dillalan mai masu zaman kansu suka ɗaga nasu farashin daga kusan N1,360 zuwa N1,400 kan lita.
Ƙarin farashin ya biyo bayan matakin da Matatar Man Fetur ta Dangote ta ɗaga farashin da take sayar da fetur ga manyan dillalai daga matakin da ake sayarwa a tashar ɗora mai, zuwa N1,350 kan kowace lita, lamarin da ke nuna tasirin tashin farashin ɗanyen mai da kuma ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa wajen samar da tare da rarraba man fetur.
Ana sa ran sabon ƙarin farashin zai jawo tashin kuɗin sufuri da na gudanar da gidaje, yayin da ’yan kasuwa da kamfanoni da ke dogaro da man fetur wajen jigilar kayayyaki, samar da wutar lantarki da sauran ayyuka za su fuskanci ƙarin kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.
Ga masu sufuri kuwa, ƙarin farashin na nufin za su ƙara kashe kuɗaɗe wajen tafiyar da motocinsu a kullum. Hakan na iya tilasta masu motocin haya, bas-bas, tasi da babura masu kafa uku ƙara kuɗin da suke karɓa daga fasinjoji domin su samu damar ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da asara ba.
Binciken da Vanguard ta gudanar ya nuna cewa wannan mataki na iya ƙara wa fasinjoji nauyi, musamman ganin yadda tuni suke kashe wani kaso mai tsoka na abin da suke samu wajen sufuri.
Ma’aikata, ɗalibai, ’yan kasuwa da sauran al’umma da ke yawan zirga-zirga zuwa wuraren aiki, makarantu, kasuwanni da cibiyoyin kasuwanci na daga cikin waɗanda ake sa ran za su fara jin tasirin ƙarin farashin.
Haka kuma, tasirin zai iya yaɗuwa zuwa sauran sassan tattalin arzikin ƙasar, domin tashin kuɗin sufuri na nufin ƙarin kuɗin jigilar abinci, kayan masarufi da kayayyakin da aka sarrafa zuwa kasuwanni.
Masu rarrabawa da ’yan kasuwa na iya tura ƙarin kuɗaɗen jigilar kayayyaki zuwa kan farashin da suke karɓa daga masu saye, wanda hakan zai iya ƙara tsadar abinci da sauran muhimman kayayyaki.
Haka kuma, iyalan da ke amfani da janareta masu amfani da fetur za su iya fuskantar ƙarin kuɗin samar da wutar lantarki a gidajensu.
Ga ƙananan masana’antu da matsakaitan ’yan kasuwa, haɗuwar tashin farashin fetur, sufuri da wutar lantarki na iya ƙara rage musu ribar da suke samu.
Masana’antu, ’yan kasuwa, kamfanonin jigilar kayayyaki, gidajen abinci da sauran harkokin kasuwanci da ke dogaro da man fetur wajen samar da kayayyaki, rarrabawa ko samar da wutar lantarki a matsayin madadin na iya sake duba kuɗaɗen gudanar da ayyukansu, wasu kuma su ƙara farashin kayayyakin da suke sayarwa.
Saboda haka, lamarin na iya ƙara haifar da hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka, yayin da ƙarin kuɗaɗen makamashi da sufuri ke shafar farashin sauran abubuwan da ake amfani da su a yau da kullum.
Da yake magana da Vanguard ta wayar tarho, Shugaban ƙasa na ƙungiyar Masu Samar da Ayyukan Mai da Iskar Gas ta Nijeriya (OGSPAN), Mazi Colman Obasi, ya ce babban abin da ya jawo wannan sabon tashin farashin shi ne ƙaruwa mai yawa da farashin ɗanyen mai ya yi a kasuwannin duniya. Ya ce hakan ya ƙara kuɗin da ake kashewa wajen samar da kayayyakin man fetur da kuma sauya tsarin tattalin arzikin samar da man a cikin gida.
Obasi ya bayyana cewa, saboda an sassauta dokokin kasuwar man fetur ta Nijeriya, farashin da ake sayar da fetur a gidajen mai yana ƙara dogaro da farashin ɗanyen mai a duniya, kuɗin tace man fetur, farashin jigilar man, canjin kuɗi da sauran kuɗaɗen da ke tattare da samarwa da rarraba man.
Ya ce idan farashin ɗanyen mai ya ci gaba da kasancewa sama da dala 100 kan ganga ko kuma ya ƙara tashi, farashin fetur a Nijeriya na iya ƙara fuskantar matsin lamba. A cewarsa, abin da ya fi damun masu sufuri a nan take shi ne ƙarin kuɗin da suke kashewa wajen tafiyar da motocinsu, yayin da fasinjoji za su fuskanci ƙarin kuɗin hawa.
Ya ƙara da cewa iyalai za su ƙara kashe kuɗaɗe wajen sufuri, abinci da wutar lantarki, yayin da ’yan kasuwa kuma za su fuskanci ƙarin kuɗaɗen jigilar kayayyaki, samarwa da makamashi.
Obasi ya ce idan tashin farashin ɗanyen mai ya ci gaba, matsin tattalin arzikin na iya ƙara yaɗuwa zuwa sauran sassan tattalin arzikin Nijeriya, lamarin da zai ƙara tsananta matsalar tsadar rayuwa da kuma wahalar gudanar da kasuwanci.
Tun da farko, Daraktar Zartarwa ta ƙungiyar Spaces for Change, Victoria Ibezim-Ohaeri, ta ce abin da ya fi damun iyalai a halin yanzu shi ne yiwuwar ƙarin kuɗin sufuri da abinci. Ta ce ƙarin kuɗin fetur da jigilar kayayyaki na iya ƙara kuɗin da ake kashewa wajen motsa mutane da kayayyaki, yayin da gidaje da ’yan kasuwa da ke amfani da janareto masu amfani da fetur ko dizal za su fuskanci ƙarin kuɗin makamashi. A cewarta, irin wannan matsin lamba na iya ƙara rage ƙarfin sayen kayayyaki na ’yan Nijeriya, musamman masu ƙaramin da matsakaicin matsayi na samun kuɗi.
Ta ce, a halin yanzu, yawan hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya a Nijeriya ya kai kashi 15.43 cikin 100, yayin da hauhawar farashin abinci ya kai kashi 20.31 cikin 100, kamar yadda Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana.
