Wasan neman shiga AFCON: Osimhen ba zai samu buga wa Super Eagles ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan wasan gaba na Super Eagles Victor Osimhen ba zai samu damar wakiltar Nijeriya ba a wani ɓangare na wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON) na 2027 sakamakon fama da raunin ƙwanji.

Sashen yaɗa labaran Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ne ya tabbatar da wannan labari a ranar Asabar cikin wata sanarwa, inda ya ce ɗan wasan na ƙungiyar Galatasaray na fama da jinkirin warkewa, inda hakan ke nufin ba zai kasance cikin tawagar Nijeriyar ba.

Da fari an sanya sunan ɗan wasan cikin jerin ‘yan wasan da za su wakilci Nijeriya a wasannin da tsammanin zai warke kafin lokacin, amma daga bisani aka samu tabbatacin ba zai samu shiga ba a lokacin da ya rasa buga wa Galatasaray wasanta da Trabzonspor a ƙarshen mako.

Osimhen ya samun wannan rauni ne a lokacin da yake wakiltar Galatasaray a makonnin da suka gabata, lamarin da ya sanya shi a halin jinya na tsawon lokaci.

A yanzu dai Super Eagles za ta nemi wani zaɓi kasancewar zakaran ɗan wasanta na gaban na fama da jinya yayin da take shirin fafatawa a wasannin neman gurbin.

By Babaji

Leave a Reply