
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu bayan shafe shekaru 77 a duniya.
Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga Satumba, 2026 a wani asibitin Birtaniya, kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito.
Saidai ba a samu cikakken bayani ba kan yadda al’amarin ya kasance, duk da wasu majiyoyin iyalansa sun ya yi fama jinya mai tsanani gabanin rasuwarsa.
Gwamna Usman Ododo na jihar mai ci a yanzu ya miƙa saƙonsa na ta’aziyya ga iyalan tsohon gwamnan. Ya bayyana shi a matsayin ɗan siyasar da ya bayar da gudummawa masu amfani a fagagen siyasa da kasuwanci.
Ododo ya kuma tunatar da haɗuwarsa ta ƙarshe da marigayin a watan Maris ɗin 2024 yayin wani zama da ya haɗa masu ruwa a tsaki a siyasa a Ƙaramar Hukumar Omala.
