Mutuwar matasan Neja: ‘Yan sanda sun rufe sabuwar hedikwatar Sibil Difens yayin da sabon kwamanda ya kama aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Neja ta sanar da rufe sabon ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) na Jihar Neja domin fara bincike kan abin alhinin mutuwar masu haƙar ma’adinai a ofishin a ranar 17 ga Satumba, 2026.

Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da haka a wata sanrwa da ya aike wa Blueprint.ng a ranar Lahadi, inda ya ce hakan wani ɓangare ne na biyayya ga umarnin Sufeto-Janar na rundunar, Olatunji Rilwan Disu.

Ya ce, an aiwatar da hukuncin ne a lokacin da Kwamishinan ‘yan sandan, Adamu Abdullahi Elleman, ya umarci a tura jami’an Atisayen Flush domin dawo rufewa da kula da lamarin yayin d Maitaimakin Kwamishina na ɓangaren manyan laifuka (SCID) Minna, kuma ya fara bincike kan al’amarin.

A cewar, kwamishinan ya tabbatar wa iyalan waɗanda al’amarin ya rutsa da su da sauran jama’a cewa ana gudanar da bincike bisa tsari tare da ƙoƙarin gano haƙiƙanin yadda al’amarin ya kasance da fitar da sakamakon a kai.

Tuni dai aka aike da Abdullahi Salisu Kabara zuwa jihar domin ya maye gurbin Suberu Aniviye a matsayin kwamandan NSCDC na Neja.

Al’amarin mutuwar matasan ya janyo zanga-zanga, mabambanta bincike a hukumance, dakatarwa da umarnin shugaban ƙasa da kuma kiraye-kiraye na a tabbatar da adalci daga ɓangaren al’umma.

Yayin da aka shiga halin bincike kan gano ainihin yadda al’amarin ya kasance, abubuwa da dama sun bayyana kama daga kama masu haƙar ma’adinan, dalilan mutuwarsu da abin da aka gano a Babban Asibitin Minna.

Wannan ya haifar da tambayoyi masu tsauri kan halin da aka tsare matasan, halin ofishin, adadin waɗanda aka tsare a gurin, matakin kulawar da aka ba su, abin da ya faru a daren faruwar mace-macen da kuma ko akwai sakaci, cikowa, rashin wadataccen iska domin samun numfashi, guba, cuta ko wani dalili da ya sabbaba aukuwar lamarin.

A yanzu dai babu wani dalili da za ce shi ne ainihin abin da ya sabbaba mutuwarsu a hukumance. Da fari dai NSCDC ta yi iƙirarin cewa al’amarin ya auku ne sakamakon ɓarkewar wata cuta, yayin da hedikwatarta ta ƙasa ta ƙalubalanci yanke hukunci haka ba tare da an kammala binciken gawa ba daga ɓangaren likitoci. Saidai, an fitar da wasu bayanai masu tayar da hankali daga waɗanda suka tsira, ‘yan uwa, jami’an asibiti da hukumomin gwamnati, waɗanda sun faɗaɗa adadin tambayoyin da ake da su kan abin alhinin.

Ita kuwa NSCDC reshen Jihar Neja, cewa ta yi jami’ansu sun ƙaddamar da “atisayen fallasa” a ranakun 15 da 16 ga Satumba a yankunan M.I. Wushishi Estate da ƙauyen Lokoto da ke Minna, kamar yadda Kwamandanta, Suberu Aniviye ya bayyana, inda ya ƙara da cewa sun kama mutane da dama da suke aikin haƙar ma’adinai ba bisa doka ba. Daga bisani a safiyar ranar Alhamis, ta ce an samu wasu daga cikinsu sun rasu sakamakon abin da ta kira da ɓarkewar wata cuta. Saidai ba ta bayar da ƙarin bayani kan yadda al’amarin ya faru ba.

Bayan haka ne aka samu ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira da ya nemi a sakaye sunansa, wanda ya ce an fesa wa takwarorin nasa ne wani sinadari yayin da suke cikin ɗakin ajiye mai laifi. Ya bayyana haka ne a lokacin da Gwamna Umaru Bago na jihar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo suka gana da shi tare da wasu biyu da suka tsira don jin abin da ya faru. Ya ce, su 67 ne jami’an NSCDC suka jibge a wani ɗaki. A cewarsa, matasan sun yi ta yin magiya ga jami’an na Sibil Difens cewa zafi ya dame su kuma suna buƙatar su sha wani abu, amma aka yi buris da su. Sannan ba a ba su ruwa ba kuma an hana iyalansu su kai musu ruwa ko abinci.

A nasa ɓangaren, Gwamna Bago ya ce abin da aka gano a asibitin da gidan ajiyar gawa sun ƙara haifar da waɗansu tambayoyi. A cewarsa, an ga wasu gawarwakin da kumfa a bakunansu da tartsatsin jini a jikkunansu yayin da kuma aka ga fatar wasu daga cikinsu ta fara ɗayewa. Gwamnan ya kuma caccaki Aniviye da sauran jami’an da ke bakin aiki kan abin da ya kira da rashin “imani” wajen jibge mutane masu yawa a irin wannan guri na tsawon sama da sa’o’i 24.

By Babaji

Leave a Reply