Ƙungiyar masu buƙata ta musamman ta gudanar da zaɓen shugabanni a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar masu buƙata ta musamman ta ƙasa, reshen Jihar Katsina ta gudanar da zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar na jihar Katsina ta hanyar sasanci (Consensus)

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, wanda Coordinator na ƙungiyar a shiyyar Arewa maso Yamma, Alh. Abdulhamid Amadu, ya wakilta, ya jagoranci rantsar da Zubairu Abdullahi a matsayin sabon Shugaban ƙungiyar, tare da sauran shugabanni 14.

Da yake jawabi, Alh. Abdulhamid Amadu ya taya sabbin shugabannin murna, inda ya buƙace su da su yi shugabanci bisa gaskiya, adalci da haɗin kai, tare da haɗa kai da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta rayuwar masu buƙata ta musamman.

A nasa jawabin, sabon Shugaban ƙungiyar, Zubairu Abdullahi, ya gode wa shugabannin ƙungiyar da mambobinta bisa amincewar da suka yi masa. Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Katsina bisa kulawar da take bai wa al’amuran masu buƙata ta musamman.

Zubairu ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta ƙara kula da buƙatun masu buƙata ta musamman, musamman ta hanyar samar da asibitin kutare na musamman da makarantu na masu bukata ta musamman, domin ba su damar samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya.

Ya kuma bayyana cewa sabon shugabancin zai mayar da hankali wajen haɗa kan mambobin kungiyar, inganta hulɗa da gwamnati, da samar da damarmaki ta fuskar ilimi, lafiya da dogaro da kai.

Shi ma Shugaban Kwamitin Zaɓen, Comrade Nasir Dauda, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana da fahimtar juna, inda aka bi tsarin sasanci domin samar da shugabancin da zai samu karɓuwa daga mambobin ƙungiyar.

Ya buƙaci sabbin shugabannin da su ɗauki amanar da aka dora musu da muhimmanci, tare da yin aiki domin amfanin ɗaukacin masu buƙata ta musamman.

Daga cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu a wajen taron akwai Sarkin Makafin Katsina, Alh. Kabir Muhammad Nahuta; Sarkin Kutare, Alh. Shamsudeen Ibrahim; Wakilin Mai Taimakawa Gwamnan Katsina kan Harkokin Masu Bukata ta Musamman, Dr. Adam Magaji; da Alh. Yau Rufa’i Zakka.

Dukkansu sun taya sabbin shugabannin murna tare da kira gare su da su haɗa kai, saurari buƙatun mambobi, kuma su yi aiki tukuru wajen inganta rayuwar masu buƙata ta musamman a jihar Katsina.

An rantsar da sabbin shugabannin 15, inda aka buƙace su da su yi aiki domin cimma manufofin IDEA Nigeria da kare muradun masu buƙata ta musamman a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply