Gwamnatin Kano ta goyi bayan Gwamnatin Tarayya kan hana wasu mallakar rukunin cibiyar kula da gandun daji

Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamnatin Tarayya wajen kare wani ɓangare na Sashen Cibiyar kula da Harkokin Gandun Daji (APCU) da ke yankin Janbulo a Ƙaramar Hukumar Gwale ta jihar daga yunƙurin mayar da shi mallakar masu zaman kansu.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Ɗahir M. Hashim ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano, ranar Juma’a.

Ya ce, gwamnatin jihar na goyon bayan Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, hukumomin NAGGW, NESREA da APCU wajen kare wannan muhimmiyar cibiyar muhalli ta ƙasa daga masu zaman kansu.

Dakta Hashim ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu mutane sun samu umarnin kotu da ke neman fitar da hukumomin APCU, NAGGW da NESREA daga harabar cibiyar.

Ya jaddada cewa, gwamnatin Kano na mutunta ikon kotuna, amma duk wani yunƙuri na mayar da cibiyar zuwa filayen gidaje ko kasuwanci ya saɓa da muradun jama’a.

A cewarsa, cibiyar APCU muhimmin ginshiƙi ne a yaƙi da hamada da lalacewar muhalli a jihohin Arewa, kuma bishiyoyin da ke cikinta suna rage zafin birane, inganta ingancin iska da kare muhalli daga zaizayar ƙasa.

Kwamishinan ya yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Babban Lauyan Tarayya da su sake duba batun mallakar cibiyar tare da ɗaukar matakan doka domin kare ta.

Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa mayar da hedikwatar gudanarwar NAGGW daga Abuja zuwa Kano, yana mai cewa hakan ya ƙara nuna muhimmancin Kano wajen yaƙi da hamada.

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta cigaba da bai wa hukumomin muhalli na tarayya dukkanin goyon bayan da ya dace domin kare cibiyar APCU, yana mai cewa matsayar gwamnatin jihar a bayyane take na cewa dukiyoyin muhalli na jama’a dole su cigaba da kasancewa cikin hidimar jama’a.

By Babaji

Leave a Reply