CBN ya fitar da muhimman matakai biyar don haɓaka fasahar kuɗi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa, mataki na gaba wajen bunƙasa fasahar kuɗi, wato Fintech, a ƙasar dole ne ya ta’allaƙa kan manyan manufofi guda biyar domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a wannan fanni.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Yemi Cardoso, ya bayyana hakan cikin saƙon fatan alheri da aka karanta a madadinsa yayin taron tattaunawa karo na uku kan fasahar kuɗi da bunƙasa harkokin kuɗi na shekarar 2026, wanda Business Journal ta shirya a Legas.

Cardoso, wanda Darakta mai kula da sa ido kan tsarin biyan kuɗi, Dakta Rakiya Yusuf, ta wakilta, ya ce ya zama wajibi ayyukan kuɗi ta hanyar fasaha su kasance masu aminci, inganci, adalci da kuma sauƙin amfani ga kowa.

Ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su riƙa gudanar da mu’amalolinsu cikin kwanciyar hankali, har ma a lokutan da ake samun cunkoso ko yawan amfani da tsarin biyan kuɗi.

A cewarsa, kuɗaɗen da ake caji ya kamata su kasance a bayyane, a kuma warware koke-koken kwastomomi cikin gaggawa, yayin da ake magance matsalolin mu’amalolin da suka gaza ba tare da jefa kwastomomi cikin wahala ba.

Ya kuma jaddada cewa kare tsarin daga hare-haren intanet da hana damfara nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, yana mai cewa dole cibiyoyin kuɗi su ci gaba da zuba jari a sabbin fasahohin tsaro, inganta hanyoyin kariya da kuma wayar da kan kwastomomi.

A nasa jawabin, Mataimakin Darakta a Babban Bankin Nijeriya, Babatunde Ajiboye, wanda ya wakilci Dakta Rakiya Yusuf, ya ce wani muhimmin mataki shi ne tabbatar da cewa ana gudanar da gasa cikin gaskiya da adalci, tare da bai wa dukkan kamfanonin da suka cika ƙa’idoji damar amfani da muhimman hanyoyin gudanar da tsarin biyan kuɗi.

Babban Bankin ya bayyana cewa ba zai iya cimma waɗannan manufofi shi kaɗai ba, yana mai cewa bankuna, kamfanonin fasahar kuɗi, masu gudanar da ayyukan kuɗin waya, kamfanonin sarrafa biyan kuɗi, kamfanonin sadarwa, ƙungiyoyin kare haƙƙin masu kwastamomi da kuma hukumomin gwamnati duk suna da rawar da za su taka.

CBN ya kuma nuna cewa makomar tsarin kuɗi na zamani a Nijeriya tana da haske, duba da cewa ƙasar na da matasa masu ƙwazo, masu sha’awar kasuwanci da kuma masu amfani da fasahar zamani.

Bankin ya ƙara da cewa cibiyoyin kuɗin Nijeriya sun nuna ƙwarewa wajen ƙirƙire-ƙirƙire, kuma idan aka haɗa da ingantattun dokoki, gaskiya wajen gudanar da aiki da kuma ci gaba da saka hannun jari, Nijeriya za ta iya gina tsarin kuɗi na zamani da zai zama abin koyi ga sauran ƙasashen Afirka da ma duniya baki ɗaya.

Cardoso ya yi alƙawarin cewa Babban Bankin Nijeriya zai ci gaba da goyon bayan sababbin fasahohin da ke magance matsalolin al’umma, da faɗaɗa damar samun ayyukan kuɗi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa bankin ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar mataki idan ya ga wasu halaye a kasuwa ko matsalolin gudanarwa da za su iya cutar da kwastomomi ko kuma kawo barazana ga zaman lafiyar tsarin kuɗi.

Ya ce, “Saƙonmu a bayyane yake: muna maraba da ƙirƙire-ƙirƙire, muna goyon bayan gasa ta adalci, kuma kare amincewar jama’a shi ne ginshiƙin duk abin da muke yi.”

A ƙarshe, ya yaba wa Business Journal Media Group bisa shirya taron, tare da ƙarfafa mahalarta su gabatar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen gina tsarin kuɗi na zamani mai aminci, adalci da kuma bai wa kowa damar cin gajiyarsa.

By ukarofi

Leave a Reply