Yanzu-yanzu: Gwamnati ta gayyaci Sheikh Gumi don amsa tambayoyi kan ayyukan ‘yan ta’adda

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta gayyaci fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, don ya zo ya amsa mata tambayoyi dangane da maganganunsa a kan ayyukan ‘yan ta’adda.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Idris ya ce Gumi bai fi ƙarfin doka ba, yana mai cewa ganin dacewar hakan ya sa gwamnati ta yanke shawarar ta gayyaci malamin don ya amsa mata tambayoyi.