Ɗan Nijeriya ya shiga jerin manyan ’yan wasan Tennis na duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani rahoto da Hukumar Shirya Gasar Tennis ta Duniya, ITTF, ta fitar ya nuna cewa ɗan Nijeriya Quadri Aruna ya shiga jerin manyan ’yan wasan Tennis 20 na duniya.

A cikin jadawalin da hukumar ta fitar, ɗan Nijeriyar ya samu matsayi na 19.

A jadawali 2 na baya-bayan nan da hukumar ta fitar, Aruna na matsayi na 22 bayan da ya yi rashin nasara a gasar kofin Tennis ta duniya wadda ta gudana a ƙasar Koriya.

Yayin da zakaran gasar a Nahiyar Africa Ɗan Ƙasar Masar Omar Assar, shima ya samu matsawa gaba zuwa matsayi na 16 a Duniya.

Kazalika Aruna, na ci gaba da mamayar gasar ITTF ta 2024 wadda aka fara daga ranar Litinin 15 ga watan Afrilu, inda ya lallasa Daniel Gonzalez da ci 11 da 6, 11 da 4, 11 da 6, da kuma 11 da 6.