Ƙaramar Sallah: Sarkin Fataskum, Umar Bubaram, ya hori masu hali kan taimako

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Martaba Sarkin Fataskum, Alhaji Umar Bubaram ya hori masu hali da su ci gaba da taimakon mabuƙata duba da halin da ake ciki na tsadar rayuwa a ƙasar.

Sarkin ya bayyana haka ne cikin makon da ya gabata a lokacin da yake miƙa saƙon barka da Sallah ga al’ummar Fataskum da Musulmin duniya bakiɗaya.

Alhaji Umar Bubaram ya ce a halin da ake ciki yanzu na taɓarɓarewar tattalin arziki, akwai buƙatar attajirai su dinga taimakon na ƙasa “domin ɗorewar zumunci da ƙaunar juna”.

Haka kuma mai martaba Sarkin Alhaji Umar Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya kuma jinjina wa Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni bisa ƙoƙarin da yake yi na yin adalci wa al’ummar jihar da kuma ƙoƙarin gina al’umma da samar ayyukan more rayuwa a jihar.

Sarkin ya ce haƙiƙa samun gwamna irin Mai Mala Buni ba ƙaramin arziki ba ne ga al’umma.

Ya kuma yi wa gwamnan fatan alheri a madadin Masarautar Fataskum da al’ummar jihar Yobe baki ɗaya.

Kazalika ya yi kira ga sauran shugabannin jihar da su bai wa gwamnan haɗin kai da goyon baya don ciyar da jihar gaba, inda ya bayyana cewa “ci gaba ba ya samuwa sai da bada goyon baya da kuma shawarwari masu kyau.”

Mai Martaba Umar Bubaram ya yi kira ga matasan Potiskum ta su zauna lafiya da junansu, kada su zama masu tada fitina da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Kazalika Sarkin ya yi kira ga malaman addini da su ci gaba da faɗakar da al’umma zuwa ga addinin Allah.