Atiku da Wike sun halarci babban taron jam’iyyar PDP a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Laraba ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar da ministan babban birnin tarayya, Nyesome Wike, suka halarci taron jam’iyyar PDP na ƙasa a Abuja gabanin kwamitin zartarwa na jam’iyyar na ƙasa.

Wannan dai shi ne karon farko da tsohon gwamnan jihar Ribas zai halarci taron jam’iyyar PDP tun bayan zaɓen shugaban ƙasa a bara.

Wike dai ya samu saɓani da shugabannin jam’iyyar PDP kuma bai goyi bayan zaɓen Abubakar da jam’iyyar ta yi ba a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaven bara.

Baya ga adawarsa da yaƙin neman zaɓen Atiku a zaɓen, matakin da Wike ya ɗauka na karɓar muƙamin minista a majalisar ministocin shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya ƙara dagula rashin jituwar da ke tsakaninsa da masu ruwa da tsaki a ɓangaren.

Wannan taron jiga-jigan jam’iyyar na ɗaya daga cikin jerin tarukan da ’yan jam’iyyar PPD ke yi, gabanin taron na NEC, inda za a tattauna muhimman shawarwarin da suka shafi shugabancin jam’iyyar da sauran batutuwan da suka kawo barazana ga haɗin kan jam’iyyar.

Gabanin taron, dukkan gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun yi wata ganawar sirri a masauƙin gwamnan Akwa Ibom da ke Abuja.

Gwamnonin da aka gani a taron sun haɗa da Sheriff Oborevwori (jihar Delta), Douye Diri (jihar Bayelsa), Siminalayi Fubara (jihar Ribas), Bala Muhammed (jihar Bauchi), Umo Eno (jihar Akwa Ibom), da Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa da dai sauransu.

Taron ya ƙunshi gwamnoni da shugabannin majalisar dokokin ƙasar da aka zava a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, da wasu mambobin kwamitin amintattu da wasu mambobin kwamitin ayyuka na PDP na ƙasa (NWC).

Har ila yau, a ranar Larabar da ta gabata, shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Sanata Iyorcha Ayu, ya janye ƙarar da ya shigar, inda ya nemi ƙalubalantar tsige shi a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

An kuma yi imanin yunƙurin nasa na da nasaba da babban taron jam’iyyar na ƙasa da ke tafe.

Kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP a gundumar Igyorov da ke qaramar hukumar Gboko a jihar Kogi ta dakatar da Ayu a shekarar 2023 bisa zargin cin zarafin jam’iyyar.

Haka kuma sun yi ikirarin cewa Ayu ba ya biyan haƙƙoƙinsa na zama ɗan majalisa kuma bai kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamna da na ’yan majalisar dokoki da aka yi a jihar Benuwai a ranar 18 ga watan Maris.

Da ya ke rashin gamsuwa da matakin da jam’iyyar ta ɗauka, Sanata Ayu ya garzaya kotu domin ƙalubalantar tsige shi.

Sai dai wata babbar kotun tarayya a watan Yunin shekarar da ta gabata ta tabbatar da hukuncin da jam’iyyar ta yanke na korar Sanata Ayu, hukuncin da ya kai ga ɗaukaka ƙara, wanda a yanzu ya janye.