02
May
'Yan sanda sun damƙe korarren Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, kan abin da ya aikata yayain zaɓen gwamna a jihar. Kakakin 'yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata cewa, yanzu haka 'yan sanda na tsare da Yunusa-Ari. Sanarwar ta ce 'yan sanda sun cika hannu da Arin ne a Abuja, inda yake ci gaba da amsa tambaya kan dalilin da ya sa ya yi riga malam masallaci wajen bayyana sakamakon zaɓe alhali ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen yayin zaɓen cike giɓi na gwamnan jihar da ya gudana kwanan baya. Ari…