Jam’iyyar LP ta sanya 23 ga watan Mayu domin zaɓen fidda gwani na Shugaban ƙasa 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jam’iyyar Labour Party ta sanya ranar 23 ga Mayu, 2026 domin gudanar da zaɓen fidda gwani na Shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.

Mai ba shugaban riƙo na jam’iyyar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ken Asogwa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce an amince da jadawalin ne a taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) tare da halartar hukumar zaɓe ta INEC.

A cewarsa, jam’iyyar za ta gabatar da rijistar mambobinta ga INEC a ranar 15 ga Afrilu, yayin da za a gudanar da zabukan fidda gwani na gwamna, sanatoci da ‘yan majalisa a ranar 15 ga Mayu. Haka kuma, za a gudanar da babban taron jam’iyyar a ranar 11 ga Afrilu.

Jam’iyyar ta kuma tabbatar da dakatar da wasu mambobi bisa zargin rashin da’a da ayyukan da suka saba wa jam’iyya, tare da ƙarfafa rajistar mambobi ta hanyar zamani da na hannu.

Bugu da ƙari, NEC ta amince da shugabancin riƙo na Nenadi Usman tare da bayyana cikakken goyon baya gare ta.

By ukarofi