Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar tsaron fararen hula da kadarorin gwamnati ta ƙasa (NSCDC) reshen jihar Kano ta tura sama da jami’ai 3,400 a faɗin jihar domin tabbatar da tsaro kafin, yayin da kuma bayan bukukuwan Eid-el-Fitr.
Kwamandan hukumar a jihar, Hassan Mohammed Agalama, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, inda ya ce matakin na daga cikin shirye-shiryen da aka yi tun da wuri domin kare muhimman kadarorin ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan a jihar.
A cewarsa, an jibge jami’an a wuraren sallar Idi, wuraren shakatawa, kasuwanni, tashoshin mota da sauran wuraren da jama’a ke taruwa domin dakile duk wani yunkurin karya doka.
Ya ƙara da cewa an ba da muhimmanci ta musamman wajen kare muhimman ababen more rayuwa kamar na lantarki, ruwan sha, hasumiyoyin sadarwa da sauran kadarorin gwamnati.
Haka kuma, ya ce an ƙarfafa sassan tattara bayanan sirri da sa ido, yayin da aka tanadi ƙungiyoyin gaggawa da ke cikin shirin ko-ta-kwana domin amsa kiran gaggawa cikin hanzari.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da doka da oda a duk tsawon lokacin bukukuwan.
Ta kuma buƙaci al’umma da su kasance masu lura, su ba jami’an tsaro haɗin kai, tare da kai rahoton duk wani abu mai tayar da hankali ga hukumomin da suka dace. Haka zalika, an shawarci iyaye da masu kula da yara da su gargadi yaransu kan gujewa aikata laifuffuka.
Kwamandan ya tabbatar wa da al’ummar jihar Kano kudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga kowa da ya gudanar da bukukuwan cikin lumana da bin doka.
Sanarwar ta samu sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar a jihar, Ibrahim Idris Abdullahi, a madadin kwamandan jihar.
