Kammala azumin Ramadan dama ce ta addu’a don kawo ƙarshen gobara a Kano — Sarkin Kasuwar Beirut

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Sarkin Kasuwar Wayar Beirut da ke Kano, Alhaji Muhammad Inuwa Labaran, ya bayyana cewa kammala azumin watan Ramadan wata babbar dama ce ga al’umma su ƙara dagewa wajen yin addu’o’i domin samun kariya daga bala’o’i, musamman yawaitar gobara a kasuwannin jihar Kano da ma sauran sassan ƙasar.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, inda ya ce addu’a ita ce hanya mafi inganci wajen magance irin waɗannan matsaloli da ke addabar al’umma.

Ya kuma miƙa sakon jajensa ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwannin Sabon Gari, Dakata da kasuwar waya, tare da addu’ar Allah Ya mayar musu da abin da suka rasa, Ya kuma kawo zaman lafiya da yalwar arziki a Kano da ƙasa baki ɗaya.

Alhaji Inuwa Labaran ya kuma jaddada muhimmancin bin doka da oda a wannan lokaci na ƙaramar Sallah, inda ya bukaci iyaye da su kula da ‘ya’yansu, musamman yayin zirga-zirga da ziyarce-ziyarce domin gujewa haɗurra.

Ya ce duk da cewa ziyartar ‘yan’uwa da abokai al’ada ce mai kyau, ya kamata a yi ta cikin kulawa da kiyaye darussan da aka koya a watan Ramadan.

A ƙarshe, Sarkin Kasuwar ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarinsa na inganta harkokin kasuwanci da rayuwar al’umma, tare da yabawa Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, kan ƙoƙarinsa na tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya.

Haka kuma ya yabawa Hakimin Fagge, Sarkin Fadar Kano Alhaji Ado Kurawa, tare da kira ga ‘yan kasuwa da su ci gaba da bai wa gwamnati da hukumomi haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

By ukarofi