Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jigo a jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya shiga jam’iyyar, yana mai gargadin cewa zai iya zama sanadiyar gazawar haɗin kan ‘yan adawa idan bai yi haka ba kafin zaɓen 2027.
Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Tɓ, inda ya ce manyan ‘yan adawa na fara taruwa a ƙarƙashin NDC domin ƙarfafa haɗin gwiwa don kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Ya ce wasu fitattun ‘yan siyasa sun riga sun koma NDC, yana mai jaddada cewa dole ne a haɗa kai domin kawar da gwamnati mai ci. Ya kuma gargaɗi cewa idan Atiku ya ƙi shiga, hakan na iya kawo cikas ga yunƙurin haɗin kan ‘yan adawa.
A cewarsa, duk wanda ya ƙi shiga wannan yunƙuri, zai ɗauki alhakin rushewar haɗin kan da ake ƙoƙarin ginawa, tare da yin nuni da cewa hakan na iya shafar damar takararsa a zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan takarar shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, sun shiga NDC bayan ganawa da shugabannin jam’iyyar.
Sai dai, masu alaƙa da Atiku sun musanta rahotannin cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa NDC, inda mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya ce babu wata tattaunawa makamanciyar haka.
