Dan takarar APC ya fashe da kuka bayan jam’iyya ta zaɓi ɗan takara ta hanyar maslaha

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wani ɗan takarar Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC), ya fashe da kuka bayan ya rasa damar samun tikitin takara, bayan da jam’iyyar ta zaɓi ɗan takara ta hanyar maslaha (consensus).

A cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ga ɗan takarar yana kuka tare da nuna takardar fom ɗin da ya saya, yana nuna takaicinsa kan yadda aka ba wani tikitin takarar duk da irin kuɗaɗen da ya kashe a wannan tafiya.

Ya bayyana cewa ya zuba kuɗaɗe masu yawa wajen neman takarar, amma a ƙarshe aka cire shi daga jerin ‘yan takara ba tare da cimma burinsa ba.

Duk da cewa cikakken bayani kan abin da ya faru bai fito fili ba, wasu muryoyi da aka ji a bayan bidiyon sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wani yanki na Arewacin Nijeriya.

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wani mutum mai suna Abdulmajeed Abdulfatai Arikewuyo ya ja hankalin jama’a a kafafen sada zumunta, bayan wani bidiyo da aka ga yana kuka saboda gazawarsa wajen tsayawa takara a kujerar majalisar dokokin jihar Kwara.

Arikewuyo, wanda ya ce shi ma ɗan takara ne, ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda aka sanar masa cewa sunansa bai kai matakin jiha ba, duk da cewa ya kammala dukkan matakan da ake buƙata a matakin mazaba.

A cikin bidiyon mai cike da tausayawa, ya ce ya gabatar da bayanansa a matakin ƙasa (ward), inda aka tabbatar masa cewa an tura sunansa zuwa mataki na gaba domin duba cancanta.

Sai dai daga bisani, lokacin da ya je bin diddigin lamarinsa a matakin jiha, sai aka sanar da shi cewa ba a samu sunansa a cikin bayanai ba, kuma ba a taɓa tura shi ba, lamarin da ya hana shi shiga takarar gaba ɗaya.

Cikin damuwa da takaici, Arikewuyo ya fashe da kuka yayin da yake bayyana abin da ya faru, yana mai nuna rashin jin daɗinsa kan abin da ya kira gazawar tsarin gudanar da zaɓen cikin gida na jam’iyyar.

By ukarofi