Jam’iyyar NDC ta warware rikicin shugabanci na Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jam’iyyar NDC ta warware rikicin shugabanci da ya taso a reshen Jihar Kano, inda ta sake tabbatar da Husaini Isah Mai Riga a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar.

NDC ta ɗauki matakin ne bayan da Mai Riga ya zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da yunƙurin ƙwace tsarin jam’iyyar a jihar.

Rikicin ya biyo bayan shigar tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jam’iyyar.

Zuwan Kwankwaso NDC ya haifar da tashin hankali a cikin reshen Kano, inda wasu mambobi suka fara tambayar makomar shugabancin Mai Riga.

Mai Riga, wanda ya yi ƙoƙarin kare matsayinsa tun farko, ya dage cewa kujerarsa halattacciya ce, kuma ba zai sauka daga muƙamin ba sai an bi tsarin doka.

Wannan rikici ya jawo hankalin shugabancin jam’iyya na ƙasa, wanda ya kira taro na musamman a ranar Talata ƙarƙashin jagorancin uban Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Henry Dickson.

Taron, wanda Kwankwaso ya halarta tare da mataimakin shugaban NDC na Arewa maso Yamma, Injiniya Muhammad Sabo Bakin Zuwo, da sauran manyan shugabanni, ya cimma matsayar tabbatar da Mai Riga a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano.

Wasu ’yan cikin cikin gida a jam’iyyar sun bayyana cewa Kwankwaso ya amince da ci gaba da barin Mai Riga a matsayin shugaban, yayin da aka ba shi wasu muƙamai.

Bayan kammala taron, Mai Riga ya nuna godiya ga shugabannin ƙasa da al’ummar Kano bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin rikicin.

Ya kuma nemi afuwar duk wanda ya ji haushi a kwanakin baya, yana mai cewa sakamakon taron ya nuna hikimar shugabannin jam’iyya.

Haka kuma ya bayyana cewa sun cimma matsaya ta ba Kwankwaso kashi 60 cikin 100 na tsarin shugabanci, yayin da shi zai ci gaba da zama shugaban.

By ukarofi