04
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Laraba ne tsohon gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya yi alƙawarin cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba zai yi nadamar naɗa shi minista ba. Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana gaban majalisar dattawa domin tantancewa. Ya taɓa riƙe mukamin minista a zamanin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan. Da yake tunawa da yawancin ayyukan da ya yi a matsayin gwamna, Wike ya ce: "Waɗannan abubuwan za a iya cimma su idan kun jajirce kuma idan kuna da sha'awar aikin." Ya ce tsofaffin gwamnoni da dama suna sha’awar zama…