Shugaban PDP na Zamfara ya koma APC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Dokta Jamil Jibo Magayaki, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC.

Dokta Jamil ya koma jam’iyyar mai mulki ne bayan komawar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, APC.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, tsohon shugaban PDP na jihar, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bisa halin da siyasa ta ke ciki a Jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce, “Ni, Dakta Jamil Jibo Magayaki, shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ina sanar da ku a hukumance cewa na koma jam’iyyar APC.”

Ya ƙara da cewa, “Na yanke shawarar komawa APC ne bisa halin da siyasa ta ke ciki a Zamfara.

“Tana buƙatar mu haɗa kai da jam’iyyar da ta fi ƙarfi don fuskantar ƙalubalen tsaro, ci gaba da kuma shugabanci domin amfanin al’ummar jihar.”

By ukarofi