Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu sanatoci tara na Majalisar Dattawan Nijeriya sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyunsu na siyasa zuwa ADC, lamarin da ya zama zaya daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa da aka gani a majalisar a ‘yan watannin baya-bayan nan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis bayan karanta wasiƙun da sanatocin suka aike, inda suka sanar da majalisar shawarar barin jam’iyyunsu na baya.
Sanatocin da suka fice sun haɗa da Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato ta Kudu), Mohammed Ogoshi Onawo (Nasarawa ta Kudu), Binos Dauda Yaroe (Adamawa ta Kudu), Austin Akobundu (Abia ta Tsakiya), da Lawal Adamu Usman (Kaduna ta Tsakiya), waɗanda dukkansu suka fito daga PDP.
Sauran sun haɗa da Ireti Kingibe (Babban Birnin Tarayya Abuja), ɓictor Umeh (Anambra ta Tsakiya) da Tony Nwoye (Anambra ta Arewa) daga Labour Party (LP), da kuma Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu) daga APGA.
Yayin karanta ɗaya daga cikin wasiƙun a zauren majalisar, Akpabio ya bayyana cewa Tambuwal ya danganta ficewarsa daga PDP da rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar.
A cewar wasiƙar, saɓani kan shugabanci, shari’o’i a kotu da kuma rabuwar kai a matakai daban-daban sun sa ya zama da wuya ya ci gaba da gudanar da siyasa cikin PDP.
Sai dai shugabancin majalisar ya bayyana cewa za a sake nazarin batun ficewar Sanata Abaribe daga APGA, inda aka ba shi mako guda ya sake duba matsayinsa. An ɗauki wannan mataki ne bayan wasu tambayoyi sun taso kan ko hujjar da ya bayar ta cire shi daga tsarin shugabancin jam’iyyar a watan Satumbar 2025 ta cika sharuɗɗan kundin tsarin mulki na sauya jam’iyya ba tare da rasa kujerarsa ba.
Da wannan sabon sauyi, yawan sanatocin ADC a majalisar ya ƙaru. A yanzu tsarin majalisar ya nuna cewa APC na da sanatoci 85, yayin da ADC ke da 9, PDP na da 8, NNPP na da 1, NDC na da 1, APGA na da 1, sannan SDP ke da sanata 1.
Akwai kujeru uku da suka zama babu kowa a kansu sakamakon rasuwar sanatoci uku da suka haɗa da Barinada Mpigi (Ribas ta Kudu maso Gabas), Godiya Akwashiki (Nasarawa ta Arewa) da Okey Ezea (Enugu ta Arewa).
Masana siyasa na ganin wannan sauyin na daga cikin abubuwan da ke ƙara nuna motsi a siyasar Nijeriya, musamman yayin da ake ta samun sauye-sauyen jam’iyya a ƙasar tun bayan da Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban ƙasa. Duk da zargin da wasu ‘yan adawa ke yi cewa ƙasar na iya karkata zuwa tsarin jam’iyya ɗaya mai rinjaye, Tinubu ya sha musanta hakan yana mai jaddada cewa Nijeriya na ci gaba da tafiya a tsarin dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama.
Fitowar ADC a matsayin wata babbar dandalin ‘yan adawa na da nasaba da haɗakar wasu manyan ‘yan siyasa da suka rungumi jam’iyyar a watan Yulin 2025 domin ƙalubalantar APC a babban zaɓen shekarar 2027. Daga cikin fitattun ‘yan siyasar da ke cikin wannan haɗaka akwai Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai, da Daɓid Mark.
