2027: Lokacin Peter Obi bai yi ba amma mutumin kirki ne, inji Dino Melaye

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Tsohon Sanatan yankin Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawa, Dino Melaye, ya bayyana cewa har yanzu lokaci bai yi ba da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, zai jagoranci Nijeriya a matsayin shugaban ƙasa.

Melaye ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata hira da ya yi a tashar talbijin na Channels, inda ya yi bayani kan siyasar Nijeriya da kuma batun zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

A yayin hirar, Melaye ya bayyana Obi a matsayin mutum nagari kuma ɗan Nijeriya mai kima, amma ya ce a ra’ayinsa, har yanzu bai kai lokacin da zai iya zama shugaban ƙasa ba, musamman idan aka duba buƙatar haɗin kan ƙasa.

A cewarsa, duk da girmamawar da yake yi wa Peter Obi, bai ga cewa yana da irin kwarewar da za ta iya haɗa kan Nijeriya a wannan lokaci ba. 

Ya ce: “Peter Obi mutum ne nagari sosai, kuma ina girmama shi matuƙa. Na taɓa faɗa a baya cewa shi mutumin kirki ne, amma a gaskiya wannan ba lokacinsa ba ne da zai zama shugaban ƙasa.”

Dino Melaye ya taɓa zama sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma daga shekarar 2015 zuwa 2023. Kafin haka kuma ya kasance ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kabba/Ijumu a Majalisar Tarayya.

Bayan ya bar Majalisar Tarayya, Melaye ya tsaya takarar gwamnan jihar Kogi ƙarƙashin jam’iyyar PDP, amma ya sha kaye a hannun gwamna mai ci a wancan lokaci, Ahmed Usman Ododo.

A halin yanzu, Melaye na cikin haɗakar ‘yan adawa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, lamarin da ya ƙara janyo cece-kuce kan yiwuwar wanda jam’iyyar za ta tsayar takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kalaman nasa sun ƙara rura wutar muhawara a fagen siyasa, musamman kan makomar takarar Peter Obi da kuma yiyuwar samun tikitin takara daga haɗakar ‘yan adawa a babban zaɓen da ke tafe.

By ukarofi