Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada ƙudurinsa na kare tsarin dimokuraɗiyya da bin doka a ƙasa, yana mai cewa aƙidar dimokuraɗiyya ita ce ginshiƙin rayuwarsa ta siyasa wadda za ta ci gaba da jagorantar dukkan matakansa a harkokin mulki.
Shugaban ya kuma bayyana dalilin da ya sa ya amince da sanya hannu kan Dokar Zaɓe da aka yi wa kwaskwarima, inda ya buƙaci dukkan ‘yan siyasa da jam’iyyun ƙasa da su gudanar da harkokinsu cikin ƙa’idojin da doka ta tanada yayin fafatawa don neman muƙaman siyasa.
An dai sha suka daga wasu ɓangarorin adawa kan matakin da shugaban ya ɗauka na sanya hannu kan sabuwar Dokar Zaɓen shekarar 2022 da aka yi wa gyara.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba a Abuja, yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin jam’iyyar APC da kuma shugabannin ƙungiyar Jam’iyyun Siyasa (IPAC) a wani taron buɗa-baki na addinai biyu da aka shirya domin watan Ramadan da kuma azumin Kiristoci.
A cikin jawabinsa, shugaban ƙasar ya waiwayi tarihin gwagwarmayar dimokuraɗiyya a Nijeriya, inda ya jaddada buƙatar ‘yan siyasa su ba da fifiko ga zaman lafiya, daidaito da haƙuri a harkokin siyasar ƙasa.
Ya ce dimokuraɗiyyar Nijeriya ta samo asali ne daga sadaukarwar mutane da dama waɗanda suka sha tsanantawa, tsarewa a gidajen yari da kuma gudun hijira domin kawo ƙarshen mulkin soja.
Tinubu ya tuno yadda wasu daga cikin masu fafutukar dimokuraɗiyya suka haɗu a ƙarƙashin ƙungiyar National Democratic Coalition (NADECO) domin fafutukar dawo da mulkin farar hula.
Shugaban ya bayyana cewa tafiyarsa a siyasa tun farko ta ginu ne kan imani da ƙaddarar da Allah ya tanada masa, yana mai cewa sadaukarwarsa ga dimokuraɗiyya ba za ta gushe ba.
A cewarsa, kasancewarsa mai kishin dimokuraɗiyya abu ne da zai ci gaba da kasancewa a rayuwarsa har ƙarshenta, musamman wajen tabbatar da haɗin kan Nijeriya.
Tinubu ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyya yana bunƙasa ne ta hanyar bambancin ra’ayoyi da kuma gasa mai lafiya tsakanin jam’iyyun siyasa. Saboda haka, ya buƙaci shugabannin jam’iyyun siyasa su rungumi tattaunawa, muhawara mai ma’ana da girmama juna a cikin harkokin siyasa.
Ya kuma tuna lokacin da ya kasance cikin ‘yan adawa a wasu shekarun baya, yana mai cewa a wancan lokaci ya mutunta dokokin dimokuraɗiyya ba tare da barazana ga kowa ba, duk da matsin lamba da ya fuskanta.
Shugaban ya jaddada cewa ƙarfin dimokuraɗiyya yana cikin daidaito tsakanin rinjaye da kuma kare muradun ƙananan jam’iyyu.
A cewarsa, rinjaye na iya samun damar aiwatar da manufofinsu, amma kuma ƙananan jam’iyyu suna da damar bayyana ra’ayoyinsu, wanda shi ne ainihin armashin dimokuraɗiyya.
Yayin da yake bayani kan dokar zaɓe, Tinubu ya ce matakin da ya ɗauka na sanya hannu kan dokar ya samo asali ne daga girmama majalisar dokoki da kuma bin tsarin doka.
Ya ce majalisar dokoki ta amince da dokar da rinjaye mai yawa, don haka bai ga dalilin ƙin amincewa da ita ba.
A cewarsa, idan yana da wata babbar shakka ko damuwa kan dokar, da ya bayyana hakan a fili. Amma tunda babu irin wannan damuwa, sai ya zaɓi bin ƙa’idar dimokuraɗiyya da mulkin doka ta hanyar sanya hannu kan dokar.
Shugaba Tinubu ya tunatar da jam’iyyun siyasa cewa zaɓe shi ne ainihin gwajin dimokuraɗiyya, inda ya ce dole ne ‘yan siyasa su kasance a shirye su karɓi nasara ko akasin haka cikin mutunci da bin doka.
A ƙarshe, shugaban ƙasar ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a siyasar Nijeriya da su ƙara haɗa kai wajen ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma kare haɗin kan ƙasa, yayin da ƙasar ke ci gaba da gina dimokuraɗiyya fiye da shekaru ashirin da aka shafe ana gudanar da mulkin farar hula ba tare da yankewa ba.
