
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yanayi na sauyin rayuwa na dare ɗaya a watan Agustan 2024, Babangida Ibrahim ya tunatar da yadda ya rasa kansa a lokaci guda wanda ya haifar da rikicewa sama da raɗaɗil, lamarin da ya janyo tsaiko ga kwanciyar hankalinsa a wannan lokaci.
Blueprint ta ruwaito cewa, Ibrahim ya kwanta cikin ƙoshin lafiya bisa rashin sanin yana dab da shiga halin buƙatar gaggawa akan cutar ƙwaƙwalwa da ke neman jarraba tunaninsa akan rashin lafiya, imani da kuma sauyin ci-gaba a fannin harkar lafiya a Nijeriya.
A yayin da yake barci ne sai jikinsa ya fara fizga wanda hakan ya sa ya rasa hankalinsa ba tare da wani gargaɗi ba.
Matarsa Zainab tana nan a lokacin da abin fargabar ke faruwar, wadda daga bisani ta ce ya fuskanci matsalar gushewar hankali.
Wannan al’amari ya cigaba da faruwa da shi akai-akai, wanda ya kai ga ya fara danganta hakan da gajiya sakamakon yawan da ayyuka suke masa.
Akan haka ne ‘yan uwa da abokan arziƙi suka riƙa bayar da shawarwari domin nema masa magani, wanda ya kai ga yin na gargajiya ba tare da sanin haƙiƙanin abin da ke damun sa ba a kimiyyace.
Likitoci sun karɓi mara lafiyar ne bayan wasu sun garzaya da shi wani asibiti a Unguwar Maitama da ke Birnin Tarayya Abuja sakamakon faɗuwa da ya yi a gefen hanya, inda aka shiga da shi ɗakin kulawa na gaggawa.
Da fari likitoci a Maitama Clinic ɗin sun yi masa taimakon farko, sanya ido akan halin da yake ciki, sannan suka bayar da shawarar a yi bincike akan lafiyar ƙwaƙwalwarsa, wanda ya zama matakin farko na kawar da zargin abin da ke damun sa.
Wani likitan kula da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa ya bada maganin cutar gushewar hankali, wanda Ibrahim ya ɗauki tsawon watanni yana yi, inda a hankali ya fara samun sauƙi, wanda ya sa aka ga dacewar faɗaɗa bincike akan halin da yake ciki.
Bayan wani ɗan lokaci a ranar 7 ga watan Fabarairu, 2025, likitoci a Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Jabi sun yi masa aiki, inda suka cire wani ƙari a ƙwaƙwalwarsa da kuma sake daidaita kwanyarsa bisa hanyoyin da suka dace.
Tun daga lokacin Ibrahim bai sake fuskantar matsalar gushewar hankali ba ko matsalar hira ko kuma rashin iya tunani.
