Kisan Ayatollah: Ba makawa sai mun ɗauki fansa – Iran

Spread the love

*An yi mana kisan ƙare dangi, inji Mojtaba Khamenei

*Amurka ta kashe Dala biliyan 11 a kwana shida na yaƙin Iran

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce, Iran za ta ɗauki fansar mutanenta da aka kashe, ciki har da yara da ɗaliban makarantar Minab, baya ga jagoran addini, Ayatollah Khamenei da aka kashe a farkon yaƙinta da Amurka da kuma Isra’ila.

Ya bayyana hakan ne a sanarwarsa ta farko da ya fitar tun bayan da aka naɗa shi a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar wanda gidan talabijin gwamnatin ƙasar ta karanto.

“Dole ne mu nemi adalci ga mutanen Iran da suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai, za mu ɗauki fansa, ba za mu manta da jinin waɗanda aka kashe ba,” inji sanarwar.

Sabon jagoran ya kuma nemi a rufe sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya kuma jaddada cewa Iran za ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz, yana mai cewa wannan mataki na daga cikin hanyoyin da ƙasar za ta bi wajen kare muradunta.

A ranar Litinin ne aka ayyana Mojtaba Khamenei a matsayin jagoran addinin Iran na uku inda hukumomi da cibiyoyi daban-daban na gwamnatin Iran, ciki har da gwamnati da ɓangaren shari’a da na tsaro da kuma soji, suka bayyana goyon bayansu ga sabon jagoran tare da yin mubaya’a gare shi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke yawo a kafafen yaɗa labarai game da lafiyar sabon jagoran.

Rahotanni sun bayyana cewa Amurka ta kashe aƙalla dala biliyan 11 a cikin kwanaki shida na farkon yaƙin da take yi da Iran, yayin da rikicin ke ci gaba da faɗaɗa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa ‘yan majalisar dokokin Amurka sun samu bayani a wani taron sirri da aka gudanar a ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon), inda aka bayyana cewa matakin farko na yaƙin ya cinye ɗimbin makamai da kuɗaɗe.

Majiyoyi da suka halarci taron sun ce adadin kuɗaɗen da aka kashe ya kai kusan dala biliyan 11.3, sai dai wannan bai haɗa da wasu kuɗaɗen da aka kashe kafin fara kai hare-haren ba.

Rahoton ya ce hakan na nufin cewa jimillar kuɗaɗen da za a kashe a makon farko na yaƙin na iya ƙaruwa matuƙa idan aka tattara dukkan bayanan da suka shafi shirye-shiryen da aka yi kafin harin.

A wasu bayanai da aka gabatar wa Majalisar Dokokin Amurka, an bayyana cewa an kashe makamai na kimanin dala biliyan 5.6 a cikin kwanaki biyu na farko kacal na fara yakin.

Masu bincike masu zaman kansu ma sun yi ƙoƙarin ƙididdige kuɗaɗen da ake kashewa a yaƙin. Cibiyar Center for Strategic and International Studies (CSIS) da ke Washington ta ƙiyasta cewa sa’o’i 100 na farko na wannan farmaki, wanda ake kira “Operation Epic Fury,” sun kai kuɗin kimanin dala biliyan 3.7, wato kusan dala miliyan 891 a kowace rana.

Masana sun kuma bayyana cewa yawancin waɗannan kuɗaɗe ba su cikin kasafin kuɗin tsaro na baya, inda aka ce kusan dala biliyan 3.5 daga cikin kuɗaɗen ba a tsara su tun farko ba.

A wani bangare kuma, wata manhaja ta intanet mai bibiyar kudaden yakin Iran da ake kira Iran War Cost Tracker ta bayyana cewa Amurka na kashe kusan dala biliyan daya a kowace rana a wannan rikici, tare da gargaɗin cewa haƙiƙanin kuɗin na iya ƙaruwa idan aka haɗa da nauyin da zai biyo baya kamar kula da tsoffin sojojin da suka ji rauni a yaƙi.

A lokaci guda, Iran ta kara tsaurara martanin da take mayarwa. Rahotanni sun nuna cewa dakarun Iran sun kai hari kan filin jirgin sama mafi cunkoso a duniya a ranar Laraba, tare da kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasuwanci a yankin.

An kuma ruwaito cewa Iran ta kai hare-hare kan rijiyoyin mai da matatun mai a kasashen yankin Gulf, tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wacce ke daya daga cikin muhimman hanyoyin safarar man fetur a duniya, inda kusan kashi ɗaya cikin biyar na man fetur da ake safarawa a duniya ke bi ta wannan mashiga.

A ranar Alhamis, wani hari daga Iran ya haddasa gobara mai girma a tsibirin Muharraƙ na Bahrain, inda filin jirgin saman kasa da kasa na kasar yake. Hukumomi sun bukaci mazauna yankin da su zauna a cikin gidajensu domin kare lafiyarsu.

Har ila yau, wani hari da aka kai a tashar jiragen ruwa ta Basra a Iraƙ ya yi sanadin mutuwar mutum guda, tare da tilasta dakatar da ayyukan dukkan tashoshin fitar da mai na kasar.

Saboda tsananin rikicin, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UN Security Council) ya bukaci Iran da ta dakatar da hare-haren da take kai wa kasashen yankin Gulf, yana mai gargadin cewa rikicin na barazana ga samar da man fetur a duniya.

Duk da haka, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka na samun nasara a yakin. Yayin wata ziyara da ya kai jihar Kentucky a ranar Laraba, ya shaida wa magoya bayansa cewa “mun yi nasara,” sai dai ya kara da cewa Amurka za ta ci gaba da yaki har sai an “kammala aikin.”

Sai dai masana sun ce samar da hanyar fita daga wannan yaki ba zai kasance mai sauki ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda shugabancin Iran mai tsaurin ra’ayi ke ci gaba da rike madafun iko.

Rahotanni sun kuma nuna cewa, duk da kashe Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei a ranar farko ta hare-haren Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, shugabannin kasar sun ci gaba da rike tsarin gwamnati ba tare da rushewa ba.

Har zuwa yanzu gwamnatin Amurka ba ta bayyana wa Majalisar Dokoki ko jama’a tsawon lokacin da yakin zai dauka ba, ko kuma adadin kudaden da za a kashe gaba daya.

By ukarofi