Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sidi Ali, wacce ta yi fice sosai a Arewacin Najeriya sakamakon rawar da ta taka a matsayin Umma, uwa mai tausayi da hikima ga Maryam a cikin shahararren shirin fim ɗin ‘Labarina’.
Duk da cewa tana da ƙarancin shekaru, idan aka kwatanta da irin rawar da take takawa, yadda take fitowa a matsayin uwa ya sa ta samu karɓuwa da yabo daga miliyoyin masu kallo.
A wannan hira da wakilin Blueprint Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu ya yi da Rahama Sidi Ali ya yi waiwaye kan rawar da ta taka a masana’antar Kannywood, tasirin da fim ɗin ‘Labarina’ ya yi ga rayuwarta ta sana’a, yadda mutane ke kallon shekarunta, da kuma ra’ayoyinta kan aure da rayuwar ta ta wajen fim.
A sha karatu lafiya.
MANHAJA: Za ki iya ba mu tarihin rayuwarki da yadda kika fara harkar fim?
RAHAMA SIDI: An haife ni ne a ranar 22 ga watan Yulin shekarar 1989 a Jihar Kaduna. A can ne na yi karatun firamare da sakandare kafin na wuce zuwa Kaduna Polytechnic domin ci gaba da karatu. Sha’awar harkar fim ta taso ne tun ina yarinya, kuma fim ɗin farko da na fara fitowa a ciki shi ne ‘Farar Mace’. Daga nan na ci gaba da fitowa a fina-finai da shirye-shiryen talabijin daban-daban, ciki har da ‘Matar Abokina’ da ‘Kwana Casa’in’.
Mutane da dama sun fi saninki da Umma a cikin fim ɗin ‘Labarina’. Yaya muhimmancin wannan rawar da kika taka a aikin?
Babu shakka, ‘Labarina’ ya sauya min rayuwar sana’a. Duk da cewa na fito a fina-finai da dama kafin wannan lokaci, rawar Umma ta ba ni shahara fiye da yadda na taɓa samu a baya. Shirin ya sa na samu karɓuwa daga masu kallo a faɗin Arewacin Najeriya, kuma ya ba ni damar nuna ƙwarewa ta a matsayin jaruma.
Yadda kika taka rawar uwa ya sa mutane da yawa suka yi zaton kin fi shekarunki. Yaya kike kallon hakan?
Abu ne mai ban sha’awa a gare ni.
Mutane da yawa kan yi mamaki idan suka haɗu da ni a zahiri saboda suna tsammanin za su ga mace mai shekaru da yawa. Ina ganin hakan yana nuna yadda masu kallo suka nutsu da halin da nake takawa. A matsayina na jaruma, irin wannan martani yana nuna cewa na yi adalci ga rawar da aka ba ni.
Me kike ganin ya sa halin Umma ya yi tasiri sosai a zukatan masu kallo?
Umma tana wakiltar kyawawan ɗabi’u da iyalai da dama ke darajantawa, kamar soyayya, haƙuri tarbiyya, hikima da tausayi. Mutane sun ji kusanci da ita saboda tana kama da irin iyayenmu mata da ake samu a cikin al’umma. Ina ganin wannan kusancin ne ya sa halin ya kasance abin tunawa ga masu kallo.
Bayan harkar fim, masoyanki na son sanin wasu abubuwa game da rayuwarki. Me za ki gaya mana?
A halin yanzu ban yi aure ba, amma kamar kowace mace ina fatan yin aure a lokacin da ya dace.
Aure muhimmiyar cibiya ce a rayuwa, kuma na yi imani cewa komai yana faruwa ne bisa ƙaddarar Allah.
Kin taɓa cewa zai yi miki wuya ki auri ɗan fim. Me ya sa?
Na taɓa bayyana hakan a fili. Ni mutum ce mai tsananin kula da waɗanda nake so da kuma kishinsu. Saboda haka, ina ganin zai iya zama ƙalubale a gare ni in auri wanda muke sana’a ɗaya. Duk da haka, rayuwa tana da abubuwan mamaki, kuma komai na iya sauyawa da yardar Allah.
Yaya za ki bayyana dangantakarki da masoyanki?
Ina matuƙar daraja masoyana domin su ne ginshiƙin ci gabanmu a wannan sana’a. Ina ƙoƙarin mu’amala da su cikin girmamawa ko a zahiri ko ta kafafen sada zumunta. Goyon bayansu da ƙarfafawarsu na da matuƙar muhimmanci a gare ni.
Wane saƙo kike da shi ga matasan da ke son shiga Kannywood?
Ina ƙarfafa musu gwiwa da su kasance masu maida hankali, ladabi da haƙuri, domin nasara ba ta zuwa cikin dare ɗaya. Su ci gaba da koyon sabbin dabaru, su mutunta dokoki da ƙa’idojin masana’antar, sannan su yi aiki tukuru domin cimma burinsu.
Me masoyanki za su sa ran gani daga gare ki nan gaba?
Masoyana su sa ran ganin ƙarin fina-finai masu inganci da kuma ƙwazo daga gare ni.
Har yanzu ina da cikakkiyar sha’awar harkar fim, kuma zan ci gaba da ba da gudunmawa wajen bunƙasa Kannywood tare da ƙarfafa gwiwar sabbin jarumai maza da mata masu tasowa.
Madalla. Muna godiya.
Ni ma na gode.
