Kisan tubabbun ‘yan ta’adda ba daidai ba ne, inji Sheikh Gumi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi ya ƙalubalanci matakin kisan tubabbun mayaƙan ‘yan tayar da ƙayar baya, ‘yan aware da fursunonin yaƙi, yana mai cewa hakan ya saɓa wa karantarwar addini da hukunce-hukuncen dokokin ƙasa-da-ƙasa.

Gumi ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce ya dace a riƙa mu’amalantar waɗanda suka miƙa wuya ko janyewa daga rikici bisa doka a madadin ɗaukar matakin hukunci mai tsanani akansu.

Malamin ya bayyana cewa wajibi ne a riƙa yi wa shari’a biyayya wajen bin hanyoyin da ta gindaya akan kowa a madadin biye wa ƙawa-zuci ko son zuciya.

Ya yi kira da a kiyaye hukuncin doka, inda ya ce akwai hukunce-hukunce masu sauƙi akan ‘yan tayar da ƙayar baya da fursunonin yaƙi da suka ajiye makamai.

Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa, muddin aka ɗauki wani mataki a wajen hukunce-hukuncen, hakan saɓa wa dokokin jin-ƙai na ƙasa-da-ƙasa ne da kuma janyo suka daga ƙasashen duniya.

Kazalika, shehin ya ce kada a riƙa sauya shari’a da ramuwa, yana mai cewa wajibi ne yankunan dake fama da rikice-rikice su tsare adalci da sulhu da kuma girmama ‘yancin ɗan-adam.

Kalaman Sheikh Gumin na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dattawa ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirinta na gyaran hali ga tubabbun ‘yan ta’adda, inda a madadin haka ta ce a riƙa gurfanar da waɗanda aka tabbatar da laifukan ta’addanci akansu.

By Babaji

Leave a Reply