Gwamnatin Tarayya ta amince da N50,000 a matsayin sabon kuɗin jarrabawar WAEC da NECO daga 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta amince da N50,000 a matsayin sabon ƙayyadadden farashin jarrabawar WAEC da ta NECO ga ɗaliban da ke shirin kammala karatun makarantun sakandare, wanda zai fara aiki daga shekarar 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya biyo bayan buƙatar da Hukumar Shirya Jarrabawar Ɗaliban Ƙasashen Yammacin Afirka (WAEC) ta gabatar ta neman a ƙara kuɗin jarrabawar kammala sakandare (SSCE) ga ɗalibai.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ke ɗauke da kwanan wata; 18 ga Yuni, 2026 da Daraktan Ilimin Babbar Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Adeniji Ibrahim ya sanya wa hannu.

An saba biyan N27,500 a matsayin kuɗin rubuta jarrabawar, wanda ke nuna cewa farashin na yanzu ya ƙaru da kusan kaso 82.

A cewar daraktan, an cimma ɗaukar matakin ne bayan wani zama da aka gudanar a tsakanin hukumomin jarrabawa da Ministan Ilimi a ranar 31 ga Maris, 2026, inda aka tattauna buƙatar nazari akan kuɗin jarrabawar kammala karatun ɗaliban.

Ya bayyana cewa, ministan ya kuma bayar da umarnin samar da tsari guda na kayan makaranta (uniform) ga masu rubuta WAEC da NECO.

Haka kuma, ministan ya umarci a sanar da matakin ga dukkan masu ruwa da tsaki domin sanin sabon matakin da aka ɗauka da kuma inganta shirye-shiryen gudanarwa a nan gaba.

By Babaji

Leave a Reply