Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gombe ta tanadi ranar yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen farko (preliminary objections) da waɗanda ake ƙara suka gabatar a shari’ar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a zaɓen Gombe na shekarar 2027.
A zaman da aka ci gaba da yi ranar Juma’a a gaban Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, lauyan jam’iyyar PDP, Barista S. M. Yusuf, ya sanar da kotun cewa ya daidaita buƙatarsa ta hanyar gabatar da roƙon baki.
Daga nan ya amince da dukkan bayanan da ke cikin ƙarin rantsuwar da ya gabatar tare da roƙon kotun ta yi watsi da ƙarar, yana mai cewa ba ta cika ƙa’idojin doka ba bisa tanadin sashe na 115 na dokar shaidu (Evidence Act).
Shi ma lauyan Farfesa Pantami, Barista Tunde Falola, ya amince da ƙorafin farko da ya gabatar tare da takardun da suka goyi bayansa, ciki har da rantsuwar sakin layi shida da Shuaibu Usman Gwani ya yi.
Ya roƙi kotun ta yi watsi da ƙarar tun daga asali saboda rashin inganci, yana mai cewa takardun da ke gaban kotun sun tabbatar da cewa Pantami ya yi murabus daga jam’iyyar APC a ranar 19 ga Mayu, 2026, kafin ya shiga zaɓen fidda gwani na PDP.
A nasa martanin, babban lauyan mai ƙara, Chief Ekpo Ejembi Ekpo (SAN), ya shaida wa kotun cewa mai ƙarar ya shigar da rantsuwar ƙaryatawa, rubutacciyar amsa ga ƙorafe-ƙorafen farko, ƙarin rantsuwa da kuma hujjojin takardu domin ƙalubalantar buƙatun da waɗanda ake ƙara suka gabatar.
Ya roƙi kotun ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen farko da PDP da Farfesa Pantami da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) suka gabatar, yana mai cewa ba su da wani ƙarfi a doka. Haka kuma ya buƙaci kotun ta ɗora musu kuɗaɗen shari’a.
Ekpo ya kuma amince da dukkan rantsuwa, ƙarin rantsuwa da rubutattun hujjojin da aka riga aka gabatar domin goyon bayan ƙarar mai shigar da ƙara.
Bayan sauraron muhawarar lauyoyin ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ta tanadi hukunci kan ƙorafe-ƙorafen farko, inda ta ce za a sanar da ɓangarorin ranar da za a yanke hukuncin nan gaba.
