Gwamna Raɗɗa ya rantsar da sabbin masu bashi shawara

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya rantsar da Dr. Surajo Yakubu Ɓatagarawa, Abubakar Kabir Kusada, da Alhaji Ahmed Abduljalal Ɗandume a matsayin mashawarta na musamman ga gwamnatin shi, tare da zama mambobin majalisar zartarwa ta Jihar Katsina.

A jawabin shi bayan kammala rantsuwar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana waɗanda aka naɗa a matsayin mutanen da suke da ƙwarewa da gogewa, yana mai nuna fatan sa na ganin sun yi amfani da iliminsu da basirar su wajen inganta ayyukan gwamnati da samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar jihar.

Gwamnan ya buƙaci sabbin mashawartan da su gudanar da ayyukansu bisa amana, gaskiya da riƙon amana, tare da yin aiki kafada da kafada da sauran mambobin Majalisar zartarwa wajen cimma manufofin gwamnati.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Joɓe, Sakataren Gwamnati, Barr. Abdullahi Garba Faskari, shugabannin ƙananun hukumomi da sauran yan uwa da abokan arziki.

By ukarofi

Leave a Reply