
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas da jagororin jam’iyyar APC a Arewa maso Gabas, sun kare matakin Shugaba Bola Tinubu na sake ɗaukar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyarsa a zaɓen 2027 da ke cigaba da ƙaratowa.
Sun bayyana hakan a matsayin sakamakon biyayya, ƙwarewar aiki, da ƙoƙarin hidimta wa ƙasa daga ɓangaren Shettima bisa jajircewa da dattako.
Yayin da fadar shugaban ƙasar ta ce yarda da tabbacin cigaba da mulkin Tinubu akan mataimakin nasa ne suka sa shi ɗaukar matakin, Tajudeen Abbas ya ce gamsuwa da Shettima daga shugaban ne ya sabbaba haka.
Su kuwa jagororin APCn na Arewa maso Gabas sun bayyana matakin a matsayin jaddada muhimmancin shiyyarsu a dabarun siyasar Ƙasa.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai na ofishin Mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce wannan mataki ya kawo ƙarshen tsawon lokaci da aka ɗauka ana jita-jitar yiwuwar sauya Shettima da wani a muƙamin.
A cewar Nkwocha, wannan mataki ya nuna yadda Shugaba Tinubu ya gamsu da Shettima da kuma hana ‘yan adawa damar suka akan zargin rarrabuwar kai acikin gwamnatinsa.
Ya ƙara da cewa, Shettima ya nuna ƙwarewa da horo musamman wajen bayar da kariya ga gyare-gyaren da gwamnatin Tinubu ta sanya a gaba, jagorantar muhimman tattaunawa akan lamuran ƙasa ta Majalisar Tattali Ƙasa (NEC) da kuma ciyar da lamuran sabunta fata ta Renewed Hope gaba bisa tsari.
