Ruftawar zauren majalisar dokokin Gombe ya yi ajalin ma’aikataci da raunata bakwai

Spread the love

Mutum ɗaya ya rasu yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon ruftawar wani sashi na sabon ginin Majalisar Dokokin Jihar Gombe da ke ƙarƙashin gini.

Al’amarin ya faru ne ranar Juma’a bayan wani ɓangaren rufin mashigar ginin da ake ginawa ya rushe a wurin aikin.

Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta Jihar Gombe, Ɗanladi Adams, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutum ɗaya daga cikin ma’aikatan ya mutu nan take, yayin da sauran bakwai suka samu raunuka daban-daban.

Ya bayyana cewa, biyar daga cikinsu na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Jihar Gombe, yayin da sauran biyun ke samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Gombe.

Bayan afkuwar hatsarin, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ba da umarnin gaggauta gudanar da bincike domin gano musabbabin ruftawar ginin.

Haka kuma ya umarci a ɗauki nauyin jinyar dukkan kuɗaɗe waɗanda suka jikkata a sakamakon al’amarin.

Gwamnan ya kuma umarci kamfanin da ke gudanar da aikin ginin da kuma masu sa ido kan aikin su gabatar da cikakken rahoton abin da ya faru cikin sa’o’i 24, domin ba ta damar gano ainihin musabbabin hatsarin da kuma ɗaukar matakan da suka dace don kauce wa sake faruwar irinsa nan gaba.

By ukarofi

Leave a Reply